in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Faransa ta komar da jakadanta daga kasar Sham
2011-11-17 14:27:42 cri

Ministan harkokin waje na kasar Faransa Alain Juppe ya sanar a ran 16 ga wata cewa, kasar Faransa ta yanke shawarar komar da jakadanta dake kasar Sham.

Alain Juppe ya yi jawabi a wannan rana a gun taron majalisar wakilai ta kasar Faransa cewa, sakamakon tarzoma da ta barke a kwanan baya a kasar Sham, kasar Faransa ta ga tilas ta rufe ofisoshin jakadanci da hukumar al'adu na kasar Faransa dake birnin Aleppo da Latakia na kasar Sham, kuma ta komar da jakadanta dake kasar. Ya kuma kara da cewa, kasar Faransa da kungiyar kasashen Larabawa suna kokarin neman kudurin da MDD ta yi game da yanayin Sham.

Kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Faransa ya bayyana a wannan rana cewa, kasar Faransa ta nuna goyon baya ga shawarar tura 'yan kallo zuwa kasar Sham da kungiyar kasashen Larabawa ta gabatar, kuma ya nemi mahukuntan kasar Sham da su amince da kwamitin sa ido na MDD da aka kafa a watan Agusta na wannan shekara zai tafi kasar domin fara aiki.

Bugu da kari, a wannan rana kuma, ministan harkokin waje na kasar Iran Ali-Akbar Salehi ya ce, kasar Iran ta nuna adawa ga kasashen waje na sa baki kan harkokin cikin gida na kasar Sham. Ya jaddada cewa, yin shawarwari zai taka muhimmiyar rawa wajen kawo karshen rikicin da ake fama da shi. Kasar Iran tana son daukar matakai masu amfani domin taimakawa kasar Sham wajen kawo karshen rikicin.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China