in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firayin ministan Isra'ila ya ce, bai kamata ba kasa da kasa su hana Isra'ila ta dauki mataki kan Iran
2012-09-12 10:51:06 cri

Jiya ranar 11 ga wannan wata, firayin ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa, idan zamantakewar al'ummar kasashen duniya ba za su hana kasar Iran ta raya makaman nukiliya ba, to, bai kamata ba su hana Isra'ila ta dauki mataki kan kasar.

A yayin taron ganawa da manema labaran da Netanyahu ya shirya tare da takwaransa na kasar Bulgaria wanda ke yin ziyara a Isra'ila Boyko Borissov, ya ce, kawo yanzu, ba a samu sakamako ko kadan ba bayan da aka yin kokarin daidaita batun nukiliya na kasar Iran ta hanyar diplomasiya da takunkumi, har kasar Iran tana kusan samun makaman nukiliya a kai a kai, idan ba za a dauki mataki ko sanar da wa'adin karshe gare ta, to, Iran za ta cigaba da raya makaman nukiliya. Netanyahu ya jaddada cewa, kasashe wadanda suka nuna kiyayya kan lamarin daukan mataki kan Iran ba su da ikon hana Isra'ila ta dauki mataki kan Iran.

A ranar 10 ga wannan wata, kakakin fadar shugaban kasar Amurka Jay Carney ya taba bayyana amma ba kai tsaye ba cewa, kasar Amurka ba ta amince da rokon Netanyahu game da daukan mataki kan Iran bisa dalilin batun nukiliya tare kuma da jaddada cewa, a halin da ake ciki yanzu, ana da lokaci da wasu sharuda masu kyau wajen daidaita batun nukiliya na Iran cikin lumana. A ran nan, sakatariyar harkokin wajen kasar Amurka Hillary Clinton ta nuna cewa, yanzu kasar Amurka ba za ta yarda da daukan mataki kan Iran ba, ita ma ba za ta yarda da sanar da kashedin wa'adin karshe ga Iran ba, kana tana yin kokarin hana Iran ta samu makaman nukiliya ta hanyar yin shawarwari wadda ta fi dacewa a halin da ake ciki yanzu.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China