in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manyan jami'an tsaron Amurka sun kammala cinikayyar wasu makamai da Isra'ila
2013-04-23 12:35:08 cri

Wasu rahotannin baya bayan nan sun bayyana cewa, wasu manyan jami'an hukumar tsaron kasar Amurka, sun jagoranci kammala hada-hadar makamai da kasar Isra'ila, wadanda kudinsu ya kai dalar Amurka biliyan 10.

An dai ce, wannan cinikayya na da manufar karfafa tasirin rundunar sojin kasar ta Isra'ila ne, duk kuwa da halin zaman dar-dar dake wanzuwa a yankin gabas ta tsakiya.

Da yake jaddada matsayin Amurka, na ba da cikakken goyon baya ga wanzuwar kasar Yahudawa ta Isra'ila, sakataren tsaron Amurka Chuck Hagel, ya ce, cinikin makaman ya kunshi samar da na'urorin kariya ga makamai masu linzami, da kuma na'urorin lura da sufurin jiragen yaki, da kuma wasu nau'o'in jiragen yaki daban-daban.

Yayin taron zantawa da 'yan jaridu na hadin gwiwa da aka gudanar a birnin Telaviv, Hagel ya ce, wannan cinikayya ta sake bude wani sabon shafi, don gane da kyakkyawar alakar tsaro dake tsakanin kasashen biyu, za kuma ta tabbatar da karfin kariyar sararin samaniya da Isra'ila ke da shi a nan gaba.

Shi kuwa a nasa bangare, ministan tsaron kasar ta Isra'ila Moshe Ya'alon, cewa ya yi, kasarsa na fatan daukar matakan siyasa, wajen warware matsalar kasar Iran. Ya kuma nanata bukatar da ake da ita, ta dakatar da ayyukan kirar makaman nukiliya da kasar ta Iran ke aiwatarwa ba da wani bata lokaci ba.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China