Kakakin babban sakataren MDD Martin Nesirky, ya furta a ranar 15 ga wannan wata a hedkwatar MDD dake birnin New York da cewa, babban sakataren MDD Ban Ki-Moon ya bayar da sanarwa, inda ya umurci gwamnatin kasar Sham da kuma kungiyar adawa ta kasar da su nuna goyon baya ga aikin shiga tsakani da Kofi Annan ke yi, kuma ya yi kira ga gamayyar kasa da kasa da ta bada goyon baya domin lallubo bakin zaren kawo karshen rikicin kasar Sham.
Ban Ki-Moon ya bayyana a cikin sanarwar da cewa, zai bi sahun jama'ar kasar Sham wajen bukatunsu ta fannonin neman samun girmamawa da 'yanci cikin adalci. Ya nemi da a kawo karshen dukkan rikice- rikicen ,tarzoma ,da kawo karshen tashe-tashen hankula ta hanyar lumana. A wannan rana, mataimakiyar sakataren mai kula da harkokin jin kai na MDD Valerie Amos ta bayar da sanarwa cewa, MDD da kungiyar hadin gwiwar kasashen Musulmai za su tura ma'aikata zuwa yankin Homs tare da kungiyar bincike ta gwamnatin kasar Sham domin yin bincike kan yanayin da ake ciki ta bangaren aikin jin kai a yankin.(Lami)