in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AL ta bukaci kwamitin sulhu na MDD da ya dauki mataki kan shirin Isra'ila na kara gina matsugunan Yahudawa
2012-12-24 10:21:04 cri

A ranar Lahadi ne kungiyar hada kan kasashen Larabawa(AL) ta bukaci kwamitin sulhu na MDD da ya dauki matakan da suka dace don takawa Isra'ila birki game da shirinta na gina matsugunan Yahudawa, kana a tuhumi kasar ta Isra'ila game da abin da zai biyo baya kan shirinta na kara gina matsugunan.

Wata sanarwar da kungiyar ta bayar a karshen ganawar wakilanta na din-din-din, kungiyar ta yi kira ga kwamitin sulhu na MDD da ya matsawa Isra'ila lamba ta martaba kudurorin MDD wadanda suka bukaci Isra'ila da ta janye daga yankuan da ta mamaye.

Bugu da kari, kungiyar ta AL ta bukaci kwamitin sulhu da ya tuhumi Isra'ila game da abin da zai biyo baya dangane da batun warware matsalar kirkiro kasashen biyu da ake yi, duk da Allah-wadai da kasashen duniya ke yiwa shirin na Isra'ila, inda suka bukaci wakilan kasashen Larabawa da ke New York da su goyi bayan wannan mataki wajen ganin kudurin MDD da ke hana Isra'ila kara gina matsagunan Yahudawa ya yi tasiri.

A baya-bayan nan ne kasar Isra'ila ta bayyana aniyyarta na gina wasu matsugunan Yahudawa 6,000 a gabashin birnin Kudus da yammacin kogin Jordan, yankin da Palasdinawa ke da niyyar kafa kasarsu ta kansu.

Wannan yunkuri na Isra'ila ya gamu da suka daga kasashen Amurka, Rasha da kungiyar EU, baya ga kasashen Larabawa.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China