Wani mai magana da yawun MDD ya yi bayani ran Talata cewa, dakarun MDD na kokarin kwantar da hankali tsakanin Isra'ila da Syria bayan an samu rahoton aukuwar musayar wuta tsakanin sojojin Syria da 'yan tawaye a Golan, wanda wani yanki ne da ya zamo iyaka tsakanin kasashen biyu.
Martin Nesirky wanda shi ne mai magana da yawun magatakardar MDD Ban Ki-Moon, yayin bayani ga manema labarai da aka saba yi kowace rana ya bayyana cewa, an samu musayar wuta jifa-jifa tsakanin dakarun kasar Syria har ma da sojojin Syria da kuma dakarun 'yan tawaye a yankin kan iyaka na Golan.
Ya ce, wannan lamari na iya yin sanadin tabarbarewar yanayi tsakanin Isra'ila da Syria, ya kuma haifar da lalacewar yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin kasashen biyu da kuma dorewar zaman lafiya a yankin.
Hukumar sa ido kan tsagaita wuta ta MDD, UNDOF wace majalisar tsaro ta MDD ta kafa a shekarar 1974 na dauke ne da alhakin tabbatar da kiyaye yarjejeniyar kawo karshen fada tsakanin Syria da Isra'ila tare kuma da yin kiran mayar da wannan yanki ya zamo kan iyaka tsakanin kasashen biyu.
Hukumar tana gabatar da wannan aiki nata da hadin kan kasashen biyu ba tare da wata matsala ba.
Nesirky ya ci gaba da cewa, kasancewar sojoji da harkokin soja a wannan yanki na kan iyaka babban laifi ne domin ya saba da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka kulla tsakanin sojojin Syria da na Isra'ila a shekarar 1974.
Ya kara da cewa, harkokin da sojojin Syria suka yi ya hada da luguden wuta da harba makamai da motocin yaki wadanda suka sauka a kalla sau biyu a yankin da Isra'ila ke ciki.(Lami)