Mista Ban ya nuna damuwarsa kan halin da kasar Sham take ciki a yayin wani taron manema labarai bayan wata ganawarsa tare da shugaban kasar Croatia Ivo Josipovic a birnin Brijuni na kasar.
Sakatare janar na MDD ya tura wani jami'in MDD dake kula da ayyukan wanzar da zaman lafiya, Herve Ladsous a kasar Syria domin kimanta halin da ake ciki a wannan kasa.
A cewar Ban Ki-moon, matakin da kwamitin tsaro na MDD ya dauka na kara wa'adin aikin tawagar sa ido zuwa kwanaki 30 na da "manufa mai kyau"
Hakazalika shugaban majalisar dinkin duniya yayi kira ga bangarori daban daban na kasar Syria dasu "dakatar da tashe tashen hankali ba tare da wani sharadi ba". (Maman Ada)