in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Iran za ta mai da martani da karfin soja idan Isra'ila ta kai mata hari, in ji sarkin musulmi na kasar
2013-03-22 15:03:17 cri
Ran 21 ga wata, sarkin musulmi na kasar Iran Ayatollah Sayyed Ali Khamenei ya nuna cewa, idan kasar Isra'ila ta yi kuskuren kai wa kasarsa hari, to Iran za ta mai da martani ta hanyar karfin soja.

Bisa labarin da aka samu daga gidan talebijin na labaran kasar Iran, an ce, jagoran musulumci Ayatollah Sayyed Ali Khamenei ya bayyana haka ne, yayin da yake halartar taron taya murnar bikin Nowruz da aka yi a birnin Mashhad da ke arewa maso gabashin kasar Iran. Ya kuma bayyana cewa, shugabannin kasar Isra'ila su kan yi wa kasar Iran barazana kan daukar wa kasar matakan soja, idan haka ya faru to kasar Iran za ta shafe manyan biranen kasar Isra'ila na Tel Aviv-Yafo da kuma Haifa daga doron duniya.

Bugu da kari, yayin da shugaban kasar Amurka Barack Obama ya gana da firaministan kasar Isra'ila Benjamin Netanyahu a ran 20 ga wata a birnin Jerusalem, ya sake jadadda cewa har yanzu akwai damar warware batun nukiliyar kasar Iran ta hanyar shawarwari, amma ya kuma jadadda cewa, idan hanyar shawarwari ta kasa, kila kasar Amurka ta dauki wasu matakai dabam don warware wannan matsala. Mr. Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa, har yanzu an kasa dakatar da kasar Iran raya makamashin nukiliya ta hanyar yin takunkumi daga fnnin diflomasiyya da tattalin arziki, da kuma bayyana ra'ayoyin kasa da kasa, shi ya sa, ya kamata a dauki matakan soja domin karfafa karfin takunkumi kan kasar Iran. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China