in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron ministocin kudi da shugabannin manyan bankunan kasashen BRICS a birnin Washingtong
2013-04-19 16:43:30 cri

An bude taron ministocin kudi da shugabannin manyan bankunan kasashen BRICS a ran 18 ga wata a birnin Washington na Amurka, inda aka tattauna batun halin da tattalin arzikin duniya ke ciki, abubuwan da za a tattauna cikin taron G20 da kuma hadin gwiwa tsakanin mambobin kasashen BRICS dangane da batun hada-hadar kudi.

An nuna cewa, ya zuwa yanzu, ana fuskantar halin rashin tabbas a fannin tattalin arzikin duniya, kuma ana yin tafiyar hawainiya wajen bunkasuwar tattalin arziki cikin gajere lokaci. Hakan ya sa, taron ya yi kira ga kasashe masu wadata da su sa kaimi ga yin kwaskwarima da karfafa daidaita ayyukan hada-hadar kudi. A sa'i daya kuma, a kawar da banazara da aka kawo domin aiwatar da manufar kudi mai sassauci.

Ministan kudi na kasar Sin Lou Jiwei wanda ke halartar taron ya nuna cewa, Sin ta samu ci gaba mai armashi wajen yi wa tsarinta kwaskwarima a wannan fanni, yayin da kasashe masu wadata suka samu rishin ci gaba da kiki-kaka a wannan fanni, don haka in ji shi ya kamata Amurka, kasashen Turai, da Japan su gaggauta wannan aiki cikin hanzari ba tare da bin hanyar ma'auni iri biyu ba, wato su nemi sauran kasashe da suka yi kwaskwarima, amma su ma su dauki matsayin ba ruwansu . (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China