Yayin taron, masu jagorancin dandalin tattaunawa kan harkokin kasuwanci da masana'antun kasashen BRICS da aka yi a ranar 26 ga wata, za su gabatar wa shugabannin sakamakon tattaunawarsu, da zai hada da shawarwarin da suka shafi ci gaba da hadin gwiwa wajen gina kayayyakin more rayuwa, aikin hakan ma'adinai, aikin noma, sha'anin kudi, makamashi da dai sauransu. Kana shugabannin da suka halarci taron za su ba da jawabi kan sakamakon.
Bisa jadawalin da aka gabatar kafin wannan, za a sanar da labarin kafuwar kwamitin kula da harkokin kasuwanci da masana'antu na kasashen BRICS a yayin taron.(Maryam)