in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya yi kira ga bangaren 'yan kasuwa da masana'antu na kasashen kungiyar BRICS da su kara yin hadin gwiwa
2013-03-27 18:14:24 cri
A ranar 27 ga wata a birnin Durban na kasar Afirka ta Kudu, an gudanar da liyafar safe na shugabannin kasashen kungiyar BRICS da 'yan kasuwa da masana'antu, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping, shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma, shugaban kasar Brazil Dilma Rousseff da kuma shugaban kasar Rasha Vladimir Putin suka halarci liyafar.

Wakilan bangaren 'yan kasuwa da masana'antu sun bada shawara ga shugabannin kasashen kungiyar BRICS cewa, kamata ya yi kasashen kungiyar su kara yi hadin gwiwa a fannonin ayyukan more rayuwa, ma'adinai, aikin gona, hada-hadar kudi, makamashi da dai sauransu, da yin amfani da fifiko wajen bunkasa kasashen, sa kaimi ga yin ciniki da zuba jari cikin 'yanci, tinkarar matsaloli, neman yanayin ciniki mai adalci, ta haka za a samu bunkasuwa tare da samun moriyar juna. Kana suna fatan gwamnatocin kasashen kungiyar za su kara taimakawa musu ta hanyar tsara manufofi da tattara kudi da dai sauransu.

Shugaba Xi Jinping ya nuna cewa, bangaren 'yan kasuwa da masana'antu suna fuskantar sabuwar dama a yanzu, yana fatan za su yi amfani da damar, don neman samun bunkasuwa kansu da bunkasuwar tattalin arzikin kasashen kungiyar BRICS gaba daya, da kara yin hadin gwiwa a tsakaninsu da gwamnatocin kasashen don inganta kasashen kungiyar a fannin tattalin arziki.

Ban da wannan kuma, shugaba Xi ya bayyana cewa, kasar Sin a tsaye take tsayin daka kan manufar bude kofa da yin kwaskwarima, da kuma samun moriyar juna. Ban da haka kuma, gwamnatin kasar Sin tana nuna goyon bayan kamfanonin kasar da su zuba jari a sauran kasashen membobin kungiyar BRICS, sannan kuma tana maraba da sauran kamfanonin kasashen kungiyar da su zo kasar Sin da zuba jari da raya aiki. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China