in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afirka ta Kudu da Sin sun rattaba hannu kan yarjejeniyar inganta ababan kyautata rayuwa
2013-03-27 10:13:48 cri

A ranar Talata ne wani kamfanin mallakar gwamnatin kasar Afirka ta Kudu dake harkar sufuri mai suna Transnet, da bankin bunkasa na kasar Sin CDB,suka rattaba hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwa wajen inganta ayyukan samar da ababan kyautata rayuwa.

Kamfanin na Transnet ya ce, yarjejeniyar ta kunshi inganta harkar jiragen kasa da kuma na teku gami da samar da na'urorin gyare-gyare.

Bugu da kari, sassan biyu sun amince da yin hadin kai nan gaba a fuskar bincike da bunkasa dabarun sarrafawa, tallace-tallace da kuma samar da ababan kyautata rayuwa a fadin nahiyar baki daya.

A yayin bukin sa hannun da aka yi a birnin Pretoria, shugaban kamfanin Transnet Brian Molefe ya ce, wannan yarjejeniyar da aka kulla tsakanin kamfanoni na kasashen kungiyar BRICS babban abin tarihi ne wanda ke nuna amfanin kasancewa a kungiyar.

Ya ci gaba da cewa, yarjejeniyar za ta samar masu wata damar nemo kudade a yunkurinsu na neman rancen gudanar da ayyukan bunkasa kasar, ganin cewa, sun samu karin hanyoyin samun rance masu sauki kuma a fannoni dabam daban.

Molefe ya ce, yarjejeniyar na daga cikin hadin gwiwa na kasa da kasa dake da nufin bunkasa tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasashen kungiyar BRICS.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China