in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kira taron ministocin ciniki karo na uku na kasashen BRICS a Afrika ta kudu
2013-03-27 15:49:35 cri
An kira taron ministocin ciniki karo na uku na kasashen BRICS a birnin Durban na kasar Afrika ta kudu a ran 26 ga wata, wanda ya samu halartar ministocin ciniki na kasashe biyar na kungiyar BRICS, ciki hadda mataimakin ministan kasuwanci na kasar Sin Chen Jian. Bayan taron, ministocin sun ba da hadaddiyar sanarwa da kuma takardar tsarin hadin gwiwa tsakanin kasashen BRICS, dangane da ciniki da zuba jari.

Yayin taron, ministocin sun tattauna kan halin tattalin arziki da duniya ke fuskanta, da tasirin da zai kawowa kasashen BRICS, tare kuma da bayyana fatansu na kara hadin gwiwa tsakaninsu, da batun tinkarar kalubaloli a fannin tattalin arziki tare. Banda haka, suna fatan kara hadin gwiwa da daidaita matsayin da suke dauka tsakaninsu.

Chen Jian mataimakin ministan kasuwanci na kasar Sin kuma ya nuna cewa, Sin za ta ci gaba da zurfafa dangantakar dake tsakanin Sin da kasashen Afrika. Ya ce, a cikin shekaru sama da 50 da suka gabata, Sin da Afrika sun kulla dangantakar hadin gwiwa a tsakaninsu, musamman ma bayan kafuwar dandalin tattaunawar hadin kai tsakanin bangarorin biyu a shekarar 2000, kasashe mambobin sun kara hadin kai, tare da samun ci gaba,musamman a fannin cinikayya tsakani Sin da kasashen Afrika.

Nan gaba, kasar Sin za ta ci gaba da ba da taimako gwargwadon karfinta, wajen bunkasa tattalin arziki da zaman al'ummar kasashen Afrika, ciki hadda fadada hadin gwiwa tsakaninta da kasashen Afrika a fannin ciniki, da zuba jari, da raya manyan ababen more rayuwa, da ci gaba da nuna goyon baya ga bunkasuwar zaman rayuwar jama'ar nahiyar ta Afrika. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China