Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana ranar Alhamis cewa, kasarsa a shirye take ta bunkasa hadin gwiwa tsakaninta da kasashen Uganda, Mozanbique da Habasha.
Shugaba Xi ya bayyana hakan ne yayin ganawa da ya yi ta daban daban da shugaban kasar Uganda, Yoweri Museveni, shugaban Mozambique, Armando Guerbuza da kuma praministan kasar Habasha Hailemariam Desalegn.
Ya ce, kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da kasar Uganda da ma sauran kasashen Afirka domin a samu cimma shirin samar da ababan rayuwa tsakanin kasashe a fadin nahiyar.
Shugaba Museveni wanda a yanzu kasarsa ce ke rike da mukamin shugaban kungiyoyin yankuna na karba-karba a Afirka ya ce, Uganda ta dora muhimmanci kan dangantaka tsakaninta da Sin tare da nuna fatan samun karin hadin kai da taimako wajen bunkasa kasar Uganda da ma nahiyar baki daya.
A kuma ganawa da ya yi da shugaba Guerbuza na kasar Mozambique, shugaba Xi ya lura cewa, kasar Sin da Mozambique sun taimakwa juna a fafutukar neman 'yancin mulkin kai, zaman lafiya da kuma bunkasa.
Shi ma da yake magana, shugaba Guerbuza ya bayyana cewa, kasarsa a shirye take ta yi hadin gwiwa da kasar Sin, inda ya lura cewa, kamfanonin kasar Sin sun yi suna a kasar, inda kuma ana son ganin karin shigowar kamfanonin kasar Sin a fannoni kamar noma, wutar lantarki, makamashi da ababan more rayuwa a kasar ta Mozambique.
Da kuma yake ganawa da Hailemariam, shugaba Xi ya lura cewa, kasashen biyu sun bi salo iri daya a fuskar bunkasa, tare kuma da karin cewa, suna da ra'ayi iri daya kan batutuwa da suka shafi kasa da kasa da ma nahiyar Afirka.
Mr. Xi har wa yau ya taya Hailemariam murna dangane da zabensa da aka yi a matsayin shugaban kungiyar hadin kan kasashen Afirka na karba-karba a wannan karo, tare da karin cewa, Sin tana darajanta wannan kungiya, kana za ta kara himma tare da kasar Habasha wajen bunkasa dangantaka tsakanin Sin da kungiyar AU da kuma Sin da nahiyar.
A nasa bangare, Hailemariam ya ce, Habasha na dora muhimmanci kan dangatakarta da kasar Sin, kana ta dauki kasar Sin a matsayin abokiyar tafiya kuma abar koyi a fuskar bunkasa kuma a shirye take ta zamo mai ra'ayi guda da kasar Sin kan batutuwa na kasa da kasa da kuma Afirka.
Shugaban Xi ya yi dukkan ganawar ne yayin taron kasashen kungiyar BRICS jiko na biyar da ta kunshi kasashen Brazil, Rasha, Indiya, Sin da Afirka ta kudu.(Lami)