in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin Xi Jinping da shugabannin kasashen Afrika sun karya kumallo tare
2013-03-28 16:39:14 cri
A ranar 28 ga wata, a birnin Durban da ke kasar Afrika ta Kudu, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron karya kumallo tare da shugabannnin kasashen Afrika.

Shugabanni mahalartan taron sun yi musayar ra'ayi kan inganta hadin gwiwa don samun moriyar juna da sa kaimi ga samun bunkasuwa tare tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika.

A ranar 27 ga wata, an yi shawarwari karo na 5 na shugabannin kungiyar BRICS a birnin Durban dake kasar Afrika ta Kudu. Bayan shawarwarin, an yi taron tattaunawa tsakanin shugabannin kungiyar BRICS da na kasashen Afrika, inda shugabanni mahalartan taron suka tattauna batun hadin gwiwa a wajen manyan ababen more rayuwa tsakanin kasashen BRICS da kasashen Afrika.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China