Haka zalika, a halin yanzu, akwai rahotanni dake nuna cewa, kasashen biyar na BRICS sun riga sun cimma ra'ayi guda, kan samar da dallar Amurka biliyan 50 cikin hadin gwiwa don kafuwar bankin, kuma za su ci gaba da yin shawarwari kan yadda za a gudanar da ayyukan shirye-shirye, dangane da kafuwar bankin a yayin taron da za su yi a Afirka ta Kudu.
Bisa shirin da aka tsara, bankin kasashen na BRICS ba kawai zai ba da taimako wajen taruwar kudade don gina ababen more rayuwa a wadannan kasashen biyar ba ne kawai, domin kuwa ana fatan zai ba da damar zuba jari ga sauran yankunan kasa da kasa, musamman ma wadanda ke nahiyar Afirka. (Maryam)