Jakadan kasar Sin a kasar Habasha kuma wakilinta a kungiyar AU Xie Xiaoyan ya ce, kungiyar BRICS wacce ta kunshi kasashe masu tasowa a fuskar tattalin arziki a duniya za ta zamo mai tasiri ga bunkasa hadin kai tsakanin kasashe masu tasowa da kuma hadin kai tsakanin kasashe masu tasowa da na masu ci gaba.
Yayin hira da kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua, Xie ya ce, taron kungiyar BRICS jiko na biyar da ta kunshi kasashen Brazil, Rasha, Indiya, Sin da Afirka ta Kudu wanda za'a yi karo na farko a nahiyar Afirka a birnin Durban dake kusa da teku, wata muhimmiyar dama ce ta tattaunawa a kan yadda kungiyar da Afirka za su ci moriyar juna.
Ya kara da cewa, kungiyar ta BRICS tana da muhimmanci matuka saboda kashi 42 daga cikin dari na yawan mutanen duniya suna cikin kasashen ne, kana suna samar da kashi daya cikin biyar na GDP, kuma su ne ke zuba jari a kasashen waje da ya kai kashi 11 cikin dari.
Jakadan na kasar Sin ya ci gaba da cewa, taron na kungiyar BRICS da za'a yi a Durban daga 26 zuwa 27 ga watan Maris, wata dama ce ga kasashen na yin tattaunawa kan makomarsu da kuma irin rawa da za su taka a yankin da ma duniya baki daya.
Yayin taron, shugabannin na kasashen BRICS za su gana da shugabannin yankuna na nahiyar Afirka.
Xie ya kara da cewa, akwai fannoni da dama da kasashen Afirka, kungiyar AU da kungiyar BRICS za su hada kai don a samu habaka tattalin arzikin nahiyar.(Lami)