A yayin da yake halartar taron ministocin kasashen BRICS, Yang ya bayyana cewa, a bana kasashen BRICS sun sami babban ci gaba wajen yin hadin gwiwa a tsakaninsu, kuma za su samu makoma mai kyau a nan gaba. Sin ta shawarci kasa da kasa da su tabbatar da sanarwar Sanya da aikin gudanarwa da aka tsara a taron shugabannin kasashen BRICS a karo na uku, a kokarin zurfafa hadin gwiwa a tsakaninsu a fannoni daban daban da muhimman harkokin duniya, tare da shirya taron shugabannin kasashen BRICS a karo na hudu yadda ya kamata.
A yayin da yake ganawa da Olugbenga Ashiru, Yang ya furta cewa, Sin na fatan karfafa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakaninta da Nijeriya, da zurfafa hadin gwiwa tsakaninsu bisa dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka, da sa kaimi ga yunkurin bunkasa sabuwar dangantakar abokantaka a muhimman sassa a tsakaninsu, da nuna goyon baya ga kungiyar tarayyar Afirka wajen taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a nahiyar yadda ya kamata. A nasa bangare, Ashiru ya bayyana cewa, Nijeriya ta darajanta dankon zumunci a tsakaninta da kasar Sin, kuma tana tsayawa tsayin daka kan manufar kasar Sin daya taka. Tana fatan samun karfafa dangantaka tsakanin kasashen biyu, tare da yin marhabin da Sin ta fuskar zuba jari a Nijeriya. Nijeriya tana fatan karfafa hadin gwiwa a tsakaninsu a MDD da dandanlin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka, domin sa kaimi ga tabbatar da zaman lafiya da tsaro a kasa da kasa baki daya.(Fatima)