Sassaucin diplomasiyya na kungiyar BRICS dake kunshe da kasashen Brazil, Rasha, Indiya, Sin da Afrika ta Kudu zai iyar kasancewa mai moriya ga nahiyar Afrika ta fuskar hadin gwiwa, in ji wasu masu ruwa da tsaki a kasar Senegal. A cikin wani rahoton da kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua ya shirya bisa jigon sakamakon da 'yan Afrika suke jira bisa huldar hadin gwiwa tare da kungiyar BRICS, da shugabanninta suka gudanar taronsu ba da jimawa ba a kasar Afrika ta Kudu.
Sin, Indiya, Rasha, Brazil ko Afrika ta Kudu, dukkansu sun zama kasashe masu saurin bunkasuwar tattalin arziki wadanda suka kasance a halin yanzu manyan kasashe a duniya dake da tsarin diplomasiyya mai sassauci. Irin wannan tsarin diplomasiyya shi ne mai tushe a wannan lokaci, in ji Alioune Badara Diouck dake kula da hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa na Pikine, wani yankin dake birnin Dakar.
Aliou Sow, wani lauya kuma shugaban kwamitin kasa na matasan Senegal ya bayyana cewa, kasashen BRICS sun kasance bisa tushen samun moriya ta dangantakar tattalin arziki da kudi.
Shi kuma Moussa Thiam, wani 'dan jarida ya nuna cewa, ya kamata hadin gwiwa tsakanin BRICS da Afrika ya tabbatar da moriyar juna, ya zama wajibi ga wadannan kasashe da su yi koyi da yammacin duniya domin su amfana albarkatun tattalin arzikin Afrika. (Maman Ada)