Ana ci gaba da taron shugabannin kasashe membobin kungiyar BRICS karo na biyar a birnin Durban dake kasar Afirka ta Kudu a ranar 27 ga wata, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping da shugabannin kasashen Brazil, Rasha, Indiya da kuma Afirka ta Kudu suke halarta.
Taken taron shi ne "hadin gwiwa a tsakanin kasashen BRICS da na Afirka domin ci gaba da cudanya, da kuma masana'antu". Kuma shugabanni kasashen membobin BRICS din za su tattauna batutuwa biyu, wato samun bunkasuwa ba tare da yin la'akari da bambance-bambance ba da kuma yin hadin gwiwa domin habaka ci gaba da dunkulewa da kuma bunkasar masana'antu. (Zainab)