A ranar Talata 26 ga watan nan ne aka bude taron shuwagabannin kasashe mambobin kungiyar BRICS, karo na biyar a birnin Durban na Afirka ta Kudu, inda da daren wannan rana, mai masaukin baki, kuma shugaban kasar Afirka ta Kudun Jacob Zuma, ya shiryawa takwarorinsa da suka halarci taron wata liyafar girmamawa.
Taken taron na bana dai shi ne, "hadin gwiwa domin habaka ci gaba da dunkulewa, da kuma bunkasar masana'antu". Ana kuma sa ran jagororin kungiyoyin bunkasa ci gaban yankunan nahiyar Afirka, za su halarci taron na wannan karo. Inda za su tattauna da ragowar mahalarta taron kan batutuwan da suka shafi dangantakar kungiyar BRICS da nahiyar Afirka a Laraba 27 ga wata, karkashin inuwar kungiyar AU.
Hakan dai na zuwa ne a gabar da ake fatan karfafa dangantaka da cudanya tsakanin hukumomi, da kungiyoyin samar da ci gaba dake nahiyar ta Afirka.
Wannan taro zai samar da damar ganawa tsakanin wakilan, da shuwagabannin BRICS, da suka hada da shugaba Jacob Zuma na Afirka ta Kudu, da shugaba Dilma Roussef na Brazil, da shugaba Vladmir Putin na Rasha, da shugaba Xi Jinping na Sin, da kuma firaministan India Manmohan Singh. Bugu da kari, ana sa ran ministocin kudin kasashe mambobin kungiyar ta BRICS za su rattaba hannu kan yarjejeniyar kafuwar bankin kungiyar a madadin kasashen nasu, bankin da ake fatan zai samar da kudaden bunkasa kayayyakin more rayuwa ga kasashe mambobi, da ma ragowar kasashe idan ya fadada. Hakan nan, ana fatan ya maye gurbin bankunan ba da lamuni na duniya, kamarsu IMF, da bankin duniya.
Har ila yau, taron zai tabbatar da kungiyar BRICS a matsayin wani jigo mai muhimmanci, a fannin samar da ci gaban zaman lafiya da lumana, da jagoranci na gari, da tsaro, tare da ikon fuskantar kalubalen dake addabar wasu yankuna duinya, ciki hadda kasar Sham, da tuni ta bukaci kungiyar ta BRICS da ta kai mata dauki, domin warware rikicin da take fuskanta ta hanyar daukar matakan siyasa.(Saminu)