Haka kuma, a yayin taron, manoma da ma'aikata na kasar sun bayyana cewa, ana sa ran kafuwar makarantar ne domin samun karin ilmi game da shuka kayayyakin gona, koyon fasahohin sarrafa kayayyakin gona da kuma yadda za a gudanar da noman cashew ta hanyoyin da suka dace, yayin da kuma yin amfani da albarkatun dajin kasar yadda ya kamata da dai sauransu, ta yadda za su iya samun karin kudin shiga ga iyalansu.
Haka kuma, sun ba da shawara cewa, ya kamata a kafa yankin noman auduga a gabashin kasar, domin habaka ayyukan gona a wannan kasa. (Maryam)