Mr. Chen, wanda ya bayyana hakan a jiya Lahadi yayin wani taron karawa juna sani game da fannin noma, ya kuma ce jimillar hatsin da kasar ta samu a bara ya karu da kaso 2.4 bisa dari, inda adadin sa ya kai tan miliyan 621, wanda ya nuna ci gaban da kasar ke samu cikin shekaru 12 a jere. Sai dai duka da hakan a cewar sa akwai bukatar shigo da karin hatsin daga ketare.
Jami'in ya kara da cewa a bara, adadin hatsin da aka shigo da shi kasar ta Sin ya kai tan miliyan 120, inda waken soya ke kan gaba da kaso 70 cikin dari na hatsin da aka sayo daga ketare.
A bara ne dai masu tsara dokokin kasar ta Sin suka jaddada aniyar su ta tabbatar da samar da isasshen abinci yayin wani taron raya karkara. Cikin kuma matakan da mahukuntan kasar ke dauka domin cimma wannan buri a cewar Mr. Chen, akwai bada kariya ga gonakin noma, da tabbatar da samun isasshiyar yabanya.(Saminu Alhassan)