Wannan dandali da aka bude ranar Asabar a Bissau, ya hada mahalarta da 'yan kasuwar kasar Sin kusan 150, musammun ma na yankin musammun na Macao na kasar Sin, da kuma kasashen Lusophone kamar kasashen Angola, Cap-Vert, Guinee-Bissau, Mozambique, Portugal da Timor Oriental domin tattauna batutuwan dangantakar tattalin arziki da kasuwanci.
Shugaban kasar Guinee-Bissau, Jose Mario Vaz ya jagoranci bikin bude wannan dandali. A cikin jawabinsa, shugaban kasar ya bukaci dukkan 'yan kasarsa da su roki Allah domin a samu yanayin zaman lafiya, kwanciyar hankali da jituwa tsakanin manyan jami'ai. A cewarsa, domin ganin harkokin zuba jarin sun tabbata da kuma ganin cigaba, dole a samu zaman lafiya tsakanin al'umma cikin kasa.
A nasa bangare, Bruno Jauad ya jaddada cewa wajibi ne ga gwamnati ta sanya kasar bisa hanyar zuba jarin kasar Sin wanda tuni ya riga ya zama wani bangare mai muhimmanci a wasu sauran kasashen Afrika, amma kuma har yanzu bai karfi ba a Guine-Bissau.
Haka kuma, ya nuna cewa dorewar tattalin arzikin kasa na dogaro da warware matsalolin siyasa dake kasancewa a Guinee-Bissau. (Maman Ada)