A jawabin sa yayin bude taron, mataimakin ministan harkokin noma na kasar Sin Qu Dongyu ya bayyana cewa, kasar Sin za ta inganta manufofin raya tambarin kamfanonin samar da amfanin gona, da sa kaimi ga canja kayan Sin zuwa tambarin Sin.
Kaza lika Qu Dongyu ya bayyana cewa raya tambarin kamfanonin samar da amfanin gona na bukatar zamanintar da sana'ar ta noma. Kuma kasar Sin kasa ce mai girma a fannin aikin gona, kana wasu nau'oin kayayyakin amfanin gona da Sin ta samar ya kai matsayin farko a duniya, an kuma rasa wasu tambarin amfanin gona da suke da karfi a kasuwar duniya.
Ya ce domin raya tambarin amfanin gona na kasar Sin, kamata ya yi a yi amfani da kasuwa, da kuma hidimar da gwamnatin kasar ke bayarwa. Game da hakan, gwamnatin kasar tana iya sa kaimi a fannin hadin gwiwa tsakanin ta da kasashen duniya, wajen kafa dandalin hadin gwiwa a tsakanin kasa da kasa, da sauran yankuna a wannan fanni. (Zainab)