A cikin sanarwar Ban ya kalubalanci bangarori daban daban da abin ya shafa na Guinee-Bissau da magoya bayansu da su dauki matakan da suka dace, don hana tsanantar rikici, kana da warware rikicin ta hanyar gudanar da tattaunawa.
Ban ya kuma cewa, rikicin siyasar da ake ta yi a kasar Guinee-Bissau ya kawo tasiri mai tsanani ga ayyukan hukumomin kasar, kana da kawo illa ga bunkasuwar tattalin arziki da zaman al'ummar kasar. Saboda haka, Ban ya yi kira ga bangarori daban daban da rikicin ya shafa da su mai da hankali kan moriyar jama'ar kasar, tare kuma da daukar matakai bisa tsarin mulkin kasa, domin kawo karshen yanayi mai tsanani da ake ciki a kasar.
A ranar 26 ga wata, shugaba Jose Mario Vaz ya nada Baciro Dja firamimnistan kasar. Wannan ne karo na biyu da aka nada shi firaminista a cikin shekara guda. Saidai wannan nadin nasa bai samu amincewa daga wajen jam'iyyar da Baciro Dja yake ciki ba wato PAIGC. A sakamakon haka, magoya bayan jam'iyyar fiye dari sun taru a gaban fadar shugaba don nuna kin amincewarsu. A kafin haka dai, ba a cimma matsaya guda kan batun zaben firaministan ba a cikin jam'iyyar PAIGC.