A cewarsa, cigaban tattalin arzikin kasar zai iya karuwa inda ba a samu rikicin siyasa ba da ya janyo rushe gwamnatin Domingos Simoes da shugaban kasar ya yi. Dalilin wannan rikici wanda ya samo tushe daga rashin jituwa tsakanin faraminista da shugaban kasa, kasar Guinee-Bissau ta tsaya fiye da wata guda ba tare da gwamnati ba. (Maman Ada)