in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Muhimmancin shawarar ziri daya da hanya daya ga ci gaban duniya
2019-05-02 15:06:18 cri

Shawarar ziri daya da hanya daya, shawara ce da shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya gabatar a shekarar 2013. Da farko shawarar ta mayar da hankali ne kan zuba jari a fannin ababan more rayuwa, ilimi, gine-gine, hanyoyin mota da layin dogo, rukunin gidajen kwana, tashoshin samar da wutar lantarki, da sauran muhimman fannoni da dan-Adam ke bukata.

Bayanai na nuna cewa, shawarar ta kasance tsarin da ya gudanar da ayyukan more rayuwa da zuba jari a mafi girma a tarihi, inda ya shafi sama da kasashe 68, ciki har da kaso 65 cikin 100 na yawan al'ummar duniya, da kaso 40 cikin 100 na ci gaban GDPn duniya a shekarar 2017.

Shawarar "ziri daya da hanya daya" ta magance gibin ababen more rayuwa, kana tana da karfin bunkasar tattalin arzikia yankin Asiya da fasifik da yankunan tsakiya da gabashin Turai. Masana sun yi imanin cewa, shawarar tana da muhimmanci wajen bunkasa alakar kasa da kasa. Kuma yanzu haka, akwai kasashe sama da 120 da kungiyoyin kasa da kasa sama da 28 da suka sanya hannu kan shawarar.

An kuma sanya shawarar cikin muhimman takardun manyan hukumomin kasa da kasa misali, MDD, kungiyar G20, kungiyar raya tattalin arzikin Asiya da Fasifik da kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai da sauransu.

Duk da sauye-sauye da yanayi na rashin tabbas da ra'ayin ba da kariya ga harkokin cinikayya da ra'ayi na kashin kai da duniya ke fuskanta a halin yanzu, shawarar da kasar Sin ta gabatar, wata dama ce da sauran kasashe za su amfana da irin ci gaba da ma fasahohin da kasar Sin ta samu .

Shawara ce da ke mutunta da tuntubar juna da alaka ta samun nasara tare gami da nuna daidaito.

Bugu da kari, shawarar wani shiri ne da kasar Sin ta gabatar bisa buri guda da al'ummomin kasa da kasa ke da shi na samar da wadata ga duniya baki daya.

Taron kolin shawarar na biyu da ya gudana a birnin Beijing na kasar Sin, ya kara tattauna matakan raya shawarar ta yadda za ta amfani duniya baki daya. (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China