Bisa umurnin da shugaba Vaz ya gabatar a jiya, an ce, gwamnatin kasar dake karkashin jagorancin Correia ta kasa gudanar da harkokin kasar tun bayan kafuwarta cikin dogon lokaci, kuma ta rasa goyon baya daga mafi yawan membobin majalisar dokokin kasar, wannan ne babban dalilin rushe ta.
A ranar 17 ga watan Satumban bara, an nada Carlos Correia a matsayin firaministan kasar Guinea-Bissau. Sabo da membobin majalisar dokokin kasar 15 daga jam'iyyar PAIGC da firaminista Correia suna ciki, sun yi wani kawance tare da jam'iyyar PRS, inda suka kada kuri'ar rashin amincewa a majalisar dokokin kasar bayan da Correia ya hau kujerar firaministan kasar, a sabili da haka, Correia ya rasa goyon baya daga mafi yawan membobin majalisar dokokin kasar, shi ya sa ba a zartas da shirin gudanar da harkokin kasa da ya gabatar ba.(Fatima)