Shugaban kasar Guinea-Bissau Jose Mario Vaz ya zartas a ranar a Litinin da takardar sunayen jami'an sabuwar gwamnatin kasar da firaministan kasar Baciro Dja ya gabatar masa.
Sabuwar gwamnatin ta hada da ministoci 16, da sakatarorin harkokin cikin gida 15, kuma akwai mata 4 daga cikin wadannan mambobin gwamnati 31. Baya ga ministan kudi, amma an tabbatar da sauran muhimman jami'an sabuwar gwamnatin.
A gun bikin nada sabuwar gwamnatin, Jose Mario Vaz ya bukaci sabuwar gwamnatin da ta yaki da cin hanci da karbar rashawa, da kuma inganta karfin kera kayayyaki. Kana Baciro Dja ya ce, zai tattauna tare da shugaban kasa domin tabbatar da ayyuka daban daban.(Lami)