Tun a ranar 16 ga watan nan ne shugaba Vaz ya danka ikon fidda sunan wanda za a nada a matsayin firaministan kasar ga jam'iyyar ta sa. A kuma yayin wani taron hukumar siyasar kasar da ya gudana ne wakilan jam'iyyar suka jefa kuri'a, tare da yanke shawarar nada mataimakin shugaban ta na farko a matsayin firaministan kasar.
A baya Vaz ya taba nada mataimakin shugaban jam'iyyar na uku, kuma minista mai kula da majalissar dokokin kasar Baciro Dja, duk da adawar da jam'iyyar ta PAIGC ta nuna game da hakan, kana babbar kotun kasar ita ma ta bayyana nadin Dja a matsayin wani mataki da ya keta dokokin kasar. Daga bisani ne kuma Mr. Dja ya sanar da sauka daga mukamin firaministan kasar. (Bako)