Wakilan gamyyar kasa da kasa dake kasar Guinee-Bissau sun bukaci masu ruwa da tsakin Guinee-Bissau da su gaggauta shiga tattaunawa domin warware bambancin siyasar dake tsakaninsu. Kiran an yi shi ne bayan ricikin dake raba kan 'yayan PAIGC, wato jam'iyyar dake mulki bayan da majalisar dokokin kasar ta yi watsi da wani shirin gwamnati na faraminista Carlos Correia.
Ovidio Pequeno, wakilin kungiyar tarayyar Afrika (AU), kuma kakakin kawancen jami'an diplomasiyya dake wannan kasa, ya tabbatar da cewa idan babu zaman lafiya, to akwai wuya gamayyar kasa da kasa ware taimakon da ta alkawari a yayin zaman taro tsakanin masu hannu da shuni na Bruxelles. (Maman Ada)