in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta kara inganta manufofin bunkasa birane da yankunan karkara tare
2019-05-07 13:44:21 cri

A jiya Litinin 6 ga wata ne, Mr. Chen Yajun, babban direktan sashen tsara manufar neman ci gaba na hukumar raya kasa da yin kwaskwarima ta kasar Sin ya bayyana a nan Beijing, cewar bunkasa birane da yankunan karkara tare wani muhimmin karfi ne na samun karin damammakin bunkasar kasar Sin. Bisa shirin da aka tsara, kasar Sin za ta bullo da wani shirin kara inganta manufofin bunkasa birane da yankunan karkara, ta yadda za a kara bunkasa tattalin arziki da zamantakewar kasar.

Bisa labarin da wakilinmu ya tattaro a wani taron manema labaru da aka yi a ran 6 ga wata, Mr. Chen Yajun, babban direktan sashen tsara manufar neman ci gaba na hukumar raya kasa da yin kwaskwarima ta kasar Sin ya bayyana a nan Beijing, cewar kawo yanzu, kasar Sin ta samu ci gaban da ba a taba samun irinsa a tarihi ba wajen bunkasa birane da yankunan karkara. Ya zuwa yanzu, yawan manoma da suke zaune a birane ya kai fiye da miliyan 90. Sannan aikin gyara tsarin gonaki ya samu sabon ci gaba. A fili yake cewa,an sake tsawaita wa'adin hayar gonaki zuwa shekaru 30. Bugu da kari, yanzu, kasar Sin ta samu ci gaba wajen daidaita inshorar tsofaffi dake birane da na yankunan karkara, da na inshorar kiwon lafiyan cututtuka masu tsanani.

A yayin taron, Mr. Chen Yajun ya bayyana cewa, "A takaice, bisa shirye-shiryen bunkasa yankunan karkara da raya sabbin birane, za a yi kokarin rage gibin dake tsakanin birane da yankunan karkara, da kuma bambancin zaman rayuwa tsakanin mazauna da manoman yankunan karkara. Sannan za a kara mai da hankali wajen kyautata tsarin 'yancin mallakar kayayyaki bisa bukatar da ake da ita a kasuwa, ta yadda manoma da mazauna birane za su iya yin musayar kayayyakinsu cikin 'yanci, da hanzarta zamanintar da aikin gona da yankunan karkara."

Chen Yajun ya kuma bayyana muhimmin aikin da za a yi wajen bunkasa birane da yankunan karkara tare, wato za a kafa tsarin daidaita kayayyakin da ake da su a birane da kuma yankunan karkara, sannan za a fitar da ka'idojin da mazauna birane da yankunan karkara za su ci gajiyar kayayyakin more rayuwar al'umma tare. Bugu da kari, za a bullo da tsarin samar da kayayyakin yau da kullum a birane gami da yankunan karkara tare, a yayin da ake kokarin bunkasa tattalin arzikin birane da yankunan karkara a lokaci guda. Daga karshe, za a tsara manufofin tabbatar da ganin kudin shiga da manoma za su samu ya karu a kai a kai.

"Dole ne a kau da manufofi da ka'idoji wadanda suke kawo cikas ga mazauna birane da wadanda suke zaune a yankunan karkara a lokacin da suke son yin musayar kayayyaki a tsakaninsu, sannan za a karfafa gwiwar shigo da karin kayayyaki yankunan karkara, ta yadda za a tabbatar da ganin an yi amfani da kwararru da gonaki da kuma zuba jari da raya masana'antu da aikin musayar bayanai a yankunan karkara kamar yadda ya kamata."

A yayin taron manema labarun da aka yi a jiya Litinin, Madam Zhou Nan, mataimakiyar babban direktan sashen tsara manufar neman ci gaba na hukumar raya kasa da yin kwaskwarima ta kasar Sin ta bayyana a nan Beijing cewa, kasar Sin za ta yi kokarin bullo da tsarin inshorar zaman al'umma iri daya a birane da yankunan karkara. Madam Zhou Nan tana mai cewa, "Inshorar kiwon lafiya da na tsofaffi ta fi jawo hankulan mazauna birane da yankunan karkara, kana ta zama wata matsala a lokacin da kasar Sin take samun ci gaba. Sabo da haka, dole ne a hanzarta bullo da wani ma'auni da zai daidaita inshorar zaman al'umma, don tabbatar da ganin inshorar zaman al'umma ta taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da ingancin zaman rayuwar al'umma da daidaita kudin shiga da ake samu a tsakanin al'ummomi."

An kuma bayyana cewa, a lokacin da ake kokarin tabbatar da ganin mazuana birane da yankunan karkara sun ci gajiyar wasu hidimomin yau da kullum, za a yi kokarin shigar da wasu hidimomi yankunan karkara. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China