Hukumar wadda ta bayyana cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a nan birnin Beijing, ta ce a wannan shekara an samu amfanin gonan da ya kai tan miliyan 621.66.
Hukumar ta kara da cewa, cikin manyan abincin yau da kullum da aka noma sun hada da shinkafa da alkama da dawa wadanda adadinsu ya kai tan miliyan 572.25, wato an samu karin kashi 2.7 cikin 100 bisa na shekarar bara.
Mr Hou Rui babban jami'in hukumar kididdiga ta Sin ya bayyana cewa, an samu wadannan nasarori ne sakamakon manufofin da gwamnatin ta bullo da su, da amfani da fasahohi na zamani da kuma raguwar bala'u daga indallahi a wannan shekara.
Bayanai na nuna cewa, fadin filayen da aka yi amfani da su wajen noma amfanin gonan ya kai eka miliyan 113.3, wato sama da kashi 0.5 cikin 100 a kan na shekarar da ta gabata. (Ibrahim Yaya)