in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An samu ci gaba ta fuskar kyautata ingancin iska a kasar Sin
2017-03-10 13:42:03 cri

An gudanar da taron manema labarai a jiya Alhamis da yamma, bisa agogon Beijing, dangane da taron shekara shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin(NPC) da ke gudana a nan birnin Beijing, inda ministan kiyaye muhalli na kasar, Chen Jining ya bayyana cewa, tun bayan da aka aiwatar da shirin magance gurbacewar iska, an samu kyakkyawan ci gaba ta fannin kyautata ingancin iska, ya kuma kara da cewa, ma'aikatar kiyaye muhalli ta kasar za ta kara karfin hana ayyukan gurbata muhalli, kuma ko kadan ba za a yi hakuri ga ayyukan da suka lalata muhalli ba.

Daidaita batun gurbacewar iska na daya daga cikin abubuwan da ke jawo hankalin kafofin watsa labarai, a yayin manyan tarukan majalisun kasar Sin na kowace shekara, wato taron shekara shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin(NPC), da na majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa na jama'ar kasar(CPPCC).

A wannan shekara kuma, batun na ci gaba da daukar hankalin al'umma. Duk da cewa, yau shekaru uku ke nan da aka aiwatar da shirin magance gurbacewar iska, amma a shekarar da ta gabata, musamman ma a lokacin dari, an sha fuskantar matsalar gurbatar iska a sassa da dama na kasar ta Sin, lamarin da ya jawo damuwar al'umma game da ko akwai ci gaban da aka samu a aikin warware matsalar. A gun taron manema labarai da aka kira a wannan rana, ministan muhallin kasar Sin, Mr.Chen Jining ya bayyana cewa, ana samun ci gaba, kuma matakan da aka dauka daidai ne. Ya ce, "A shekarar 2016, yawan sinadarai masu guba da ke cikin iska na mita daya ya kai microgram 73, adadin da ya ragu da kashi 18% kwatankwacin na shekarar 2013. Haka kuma a birane 74, wannan adadi ya kai microgram 50 a cikin yawan iska mita daya, kuma ya ragu da kashi 30.6% idan aka kwatanta da na shekarar 2013. Ban da haka, yawan ranekun da ake samun iska mai inganci na karuwa, a yayin da ranekun da ake fuskantar gurbacewar iska na raguwa."

Duk da ci gaba da aka samu, Mr.Chen Jining ya ce, akwai sauran rina a kaba, musamman ma a game da batun samar da dumi a lokacin dari, aikin da ya kan haifar da gurbatacciyar iska. Don haka, a rahoton aikin gwamnati na wannan shekara, an tsara ayyukan da za a gudanar domin daidaita matsalar. Ma'aikatar kiyaye muhalli ta kasar Sin ita ma za ta kara karfin aikin binciken musabbabin gurbacewar iska. Ya ce, "A cikin 'yan shekarun baya, mun gudanar da bincike a birane 35, game da abubuwan da suka haddasa gurbacewar iska, kuma mun gano cewa kona kwal, da hayakin da da masana'antu ke fitarwa, da kura da ma motoci, su ne suka fi sauran sassa gurbata iska, sai dai abubuwan da suka haddasa matsalar su kan bambanta a sassa daban daban da kuma lokuta daban daban. A gaba, za mu kara karfin gudanar da bincike, don mu warware wannan matsala bisa ga ainihin dalilin aukuwarta. "

Tun bayan da aka fara aiki da sabuwar dokar kiyaye muhalli a ranar 1 ga watan Janairun shekarar 2015, aikin kiyaye muhalli bisa doka ya inganta sosai. Sai dai akwai wasu masana'antu da suke ci gaba da keta dokokin suna ta fitar da hayaki a boye. A game da wannan matsala, Mr.Chen Jining ya jaddada cewa, ko kadan ba za a nuna hakuri ga ayyukan da suke gurbatar muhalli ba. Ya ce, "Za a ci gaba aiwatar da dokar kiyaye muhalli, tare da kyautata dokokin da ka'idojin da suka shafi hakan. Za a kara karfin dakile yunkurin keta dokokin, da yanke hukunci ga wadanda suka karya dokokin, ko kadan ba za a jurewa ayyukan da suke lalata muhalli ba."(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China