170305-NPC-MARYAM.m4a
|
Duk da an gamu da kalubale da dama a shekarar 2016, kasar Sin ta cimma burinta na samun bunkasar tattalin arziki kamar yadda ta tsara. Yayin da yake gabatar da Rahoton, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya bayyana cewa, lallai akwai wasu matsalolin a fannin ci gaba da raya tattalin arziki da zaman takewar al'umma.
"Bai kamata a rage mai da hankali a kan harkar tattalin arziki da sha'anin kudi ba.Ana ci gaba da gamuwa da matsalar gurbatar muhalli mai tsanani, musamman ma matsalar hazo mai cutarwa da ake samu a kasar nan. Haka zalika, jama'ar kasar Sin na da matsaloli da dama da suka hada da samun matsuguni, neman ilmi, kiwon lafiya da kula da tsoffi da dai sauransu."
Game da yadda gwamnatin kasar a wannan karo za ta gudanar da ayyukanta a shekarar bana, domin warware wadannan matsaloli, da kuma hasashen da aka yi kan karuwar tattalin arziki na shekarar bana, firayiministan ya ce:
"Bisa hasashen da aka yi, ana sa ran samun karuwar GDP na kashi 6.5 bisa dari, kuma za a dukufa wajen samun sakamako mai kyau, domin tabbatar da samar da isassun guraben ayyukan yi tare da ba da tallafi ga al'ummomin kasar nan yadda ya kamata. Kuma, wannan hasashen da aka yi na samun karuwar GDP da kashi 6.5 bisa dari, ya dace da tsarin bunkasar tattalin arziki da kuma halin da kasar take ciki yanzu, shi ya sa, zai dace a kyautata tsarin tattalin arziki a kasar Sin, baya ga gina zaman takewar al'umma mai cike da wadata.
Kwanan baya, masu zuba jari na kasashen waje sun mai da hankali kwarai kan yin kasuwanci a kasar Sin, shi ya sa, aka bayyana cikin rahoton da gwamnati ta fidda cewa, kasar Sin za ta gaggauta gina tsarin tattalin arziki da zai bude kofa ga kasashen waje. Li Keqiang ya ce,
"Za a gyara takardar ba da shawara ga masu zuba jari na ketare kan yadda za su gudanar da ayyukansu a kasar Sin, domin kara jan hankalinsu, musamman ma a fannonin samar da hidima, kirkire-kirkire da kuma hakar ma'adinai. Kana, za a kuma karfafawa 'yan kasuwar kasashen ketare gwiwar sayar da hannun jari a kasar Sin, da kuma ba su damar shiga a dama da su a fagen raya harkokin kimiyya da fasaha. Karkashin kudurin na ci gaba da bude kofa ga kasashen waje, har da batun samar da daidaito tsakanin kamfanonin kasar Sin da na kasashen ketare, ta yadda ba za a rika bambanta su da na cikin gida ba, tare da ba su damarmaki iri daya."
Cikin shekarar 2016 da ta gabata, gwamnatin kasar Sin ta karfafa ayyukanta na warware matsalar hazo mai tsanani, amma ba a samu sakamako kamar yadda al'ummomin kasar suke fata ba, shi ya sa, a bana, gwamnatin za ta ci gaba da dukufa kan wannan aiki.
"Gaggauta aikinmu na kyautata yanayin muhalli, musamman ma yanayin iskar kasa ya kasance babban fatan jama'a, ya kuma kasance babban tushen samun dauwamammen ci gaba. Shi ya sa, ya kamata a yi amfani da dabaru na kimiyya da fasaha wajen warware matsalar daga tushe, kuma ya kamata a hukunta wadanda ba su aiwatar da ayyukan warware gurbatar iska yadda ya kamata. Bugu da kari, ana fatan ganin dukkanmu mun dauki alhakin kyautata yanayin iskar kasa, ta yadda za a kawar da matsalar gaba daya. "
Har ila yau, Firaministan Li Keqiang ya yi kira da a dukufa wajen gudanar da ayyuka yadda ya kamata.
"Ya kamata mu sauke nayuin dake kanmu yadda ya kamata, kuma mu dukufa domin cimma burin da aka tsara na samun bunkasar tattalin arziki da zaman takewar al'umma, ta yadda za mu cimma burinmu na samar da wata kasa mai wadata da kuma zaman lafiya."
Shekarar bana shekara ce ta musamman ga kasar Sin inda a nan gaba ne kuma, za a kira taron majalisar wakilan jam'iyyar kwaminis ta Sin karo na 19.(Maryam)