in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya tattauna da wakilan jama'ar kasar Sin kan batun fama da talauci
2017-03-09 13:24:56 cri

A safiyar jiya Laraba, ranar 8 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping wanda har ila yau shi ne babban sakataren kwamitin tsakiya na JKS, kana shugaban kwamitin tsakiya na rundunar sojojin kasar, ya tattauna da wakilan lardin Sichuan, a taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar NPC da ke gudana yanzu haka a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.

Sakamakon kasancewar lardin Sichuan wani lardi ne da ya dogara da ayyukan gona, don haka yadda za a yi kwaskwarima ga tsarin samar da amfanin gona, da kuma cimma nasara wajen yaki da talauci ya zama muhimmin batun da suka mai da hankali a kai.

"Yau wata rana ce ta musamman, kasancewarta ranar mata ta duniya. Don haka, a madadin kwamitin tsakiya na JKS, da majalisar gudanarwar ta kasar Sin, ina mika gaisuwa da fatan alheri ga wakilai mata masu halartar taron NPC da na CPPCC, da ma'aikata mata a yayin tarukan biyu, gami da mata daga kabilu da sassa daban daban na duk fadin kasar Sin, don taya su murnar ranar mata ta duniya."

Tawagar lardin Sichuan na da wakilai 148, daga cikinsu, yawan wakilai mata ya kai rubu'i, wadanda suka zo daga kabilun Han, Qiang, Miao, Yi, Tibet da dai sauransu. Yayin da Shugaba Xi Jinping ke yin mu'amala tare da wakilan lardin na Sichuan, ya ambaci wani batun da ya dame sa sosai.

"Na taba duba labari kan kauyen hayi na yankin Liangshan, halin zaman rayuwa da yara mazauna wurin ke ciki ya dame ni sosai. A 'yan kwanakin baya, na samu labari kan cewa, an gina sabbin matakalu na karfe a wurin, wanda ya kwantar da hankalina. Ya kamata gwamnatinmu ta kara mara baya ga lardin Sichuan wajen magance fama da kangin talauci."

Wannan kauyen da shugaba Xi ya ambata yana yankin Liangzhou da ke lardin Sichuan, sunansa Atule'er. Ga mazauna kauyen kuma, ko wane fita da shigowarsu, babu yadda za a yi, sai su hau matakalun igiyoyi da hannayensu, wadanda tsayinsu ya kai kusan kilomita daya daga kasa zuwa sama. Ga yaran kauyen kuma, suna bukatar hawa matakalun a ko wace rana don zuwa makaranta. Tun bayan da kafofin watsa labarai na kasar Sin suka ba da rahoto kan kauyen a watan Mayu na bara, kauyen Atule'er ya samu babban sauyi, inda aka yi amfani da karfe wajen gina sabbin matakalun.

Yankin Liangzhou yana kudu maso yammacin lardin Sichuan, inda ake iya samun yawan 'yan kabilar Yi, kuma ya kasance daya daga cikin yankuna 14 mafiya fama da kangin talauci a kasar Sin, har ma yawan mazauna yankin masu fama da talauci ya zarce dubu 500. Lin Shucheng, daraktan reshen JKS da ke yankin Liangshan ya yi wa shugaba Xi Jinping bayani kan yawan marasa ilimi da ke yankin, da kuma ci gaban da aka samu wajen magance matsalar fama da talauci. Lin Shucheng ya gaya masa cewa,

"A shekarar bana, za mu kara dora muhimmanci kan aikin magance fama da kangin talauci. Bisa shirin da muka tsara, za mu gina sabbin kauyuka 500, da kuma sauyawa mutane dubu 50 wurin zama, kafin zuwan lokacin damina. Banda wannan kuma, mun riga mun kaddamar da aikin gina dakunan kwana a kauyuka 166 da ke gundumomi uku, da zummar fitar da su daga kangin talauci a shekara mai zuwa."

Bisa labarin da aka samu, an ce, kawo yanzu dai, yawan mutane masu fama da talauci ya ragu daga miliyan 7.5 na shekarar 2012 zuwa miliyan 2 da dubu 720 na shekarar bara.

Da jin hakan, shugaba Xi wanda ko da yaushe ke tsayawa tsayin daka kan aniyar sa ta yaki da talauci bisa halin da ake ciki, kuma ta hanyar da ta fi dacewa ya jaddada cewa, ya kamata a ci gaba da sanya batun fitar da yankunan kabilar Yi da ta Tibet daga kangin talauci a gaban kome. Yana mai cewa,

"Abu mai muhimmanci na aikin yaki da talauci a halin yanzu shi ne, daukar matakan da suka fi dacewa da halin da ake ciki. Da maida hankali kan kananan wurare, da bincike kan wanda ke bukatar taimako, da wanda zai samar da taimakon, da ta yaya za a ba da taimakon, gami da ta yaya za a janye tsarin ayyukan ba da taimako domin a samu karfin raya kai. Duk wadannan ayyuka ana bukatar yin nazari a kansu cikin tsanake. Bugu da kari, ya kamata a dora muhimmanci kan magance batun sake shiga halin kangin talauci, da kuma karfafa karfin wadannan wurare wajen raya kansu."(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China