in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin wajen Sin ya yi bayani kan manufofin diflomasiyyar kasar Sin
2017-03-08 19:08:44 cri

A yayin taron manema labarai da aka yi a yau Laraba, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya yi bayani kan batutuwan dake janyo hankulan kasashen duniya, kamar hadin gwiwar kasa da kasa, dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka, yanayin zirin Koriya da kuma manufofin diflomasiyyar kasar Sin da dai sauransu.

A watan Mayun bana ne, kasar Sin za ta yi taron kolin hadin gwiwar kasa da kasa game da shirin "hanya daya da ziri daya", Wang Yi ya bayyana fatan kasar Sin kan wannan taro, a yayin dake ganawa da manema labarai, yana mai cewa, "Kasar Sin ce ta bullo da shirin nan na "hanya daya da ziri daya", amma kasashen duniya su ne za su ci moriyar wannan shiri. Muna kuma sa ran cimma sakamako guda uku bayan wannan taro. Na farko, a tabbatar da ra'ayi daya da sassa daban daban suka cimma domin daidaita manufofin kasa da kasa ta yadda za a samu cikin hadin gwiwa da kuma tabbatar da burinmu na samun ci gaba tare bisa kokarin kasashen duniya. Na biyu kuma, ya kamata mu gabatar da fannonin da za a fi mai da hankali wajen yin hadin gwiwa, musamman ma fannonin samar da ababen more rayuwa, zuba jari, da kuma musayar al'adu da dai sauransu. A karshe, a bullo da shirin yin hadin gwiwa na dogon lokaci da kuma yin tattaunawa kan dauwamammen ci gaban shirin "hanya daya da ziri daya", ta yadda za a gina dangantakar abokantaka a tsakanin sassa daban daban yadda ya kamata."

A lokacin da yake tsokaci kan dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasar Amurka, minista Wang ya bayyana cewa, dangantakar dake tsakanin kasashen biyu tana ci gaba cikin yanayin zaman karko, a watan Fabrairun bana ne, shugabannin kasashen biyu suka yi shawarwari ta wayar tarho, inda suka cimma ra'ayi daya game da martaba manufar "kasar Sin daya tak a duniya", da jaddada muhimmancin ci gaba da raya dangantakar kasashen biyu, Mista Wang ya kara da cewa, "A halin yanzu, kasar Sin da kasar Amurka suna dukufa wajen habaka mu'amalar dake tsakanin shugabannin kasashen biyu da kuma raya hadin gwiwar kasashen biyu bisa fannoni daban daban, kuma, kasar Sin da kasar Amurka za su zama abokan hadin gwiwa na arziki muddin za su martaba manufofin da shugabannin kasashen biyu suka cimma, wato rashin nuna kiyayya ga juna, da girmama juna da kuma yin hadin gwiwa domin cimma moriyar juna."

Game da hali mai tsanani da ake ciki a yankin Koriya, a yayin da yake ambato shawarar bangaren Sin, Mr. Wang Yi yana mai cewa, abin da ya kamata a yi cikin gaggawa yanzu shi ne kasashen Koriya ta arewa da Amurka da Koriya ta kudu su dakatar da matakan da suke dauka yanzu ba tare da bata lokaci ba.

"Shawarar bangaren Sin ita ce, da farko dai, kasar Koriya ta arewa ta dakatar da gwaje-gwajen makaman nukiliya da take yi, a waje daya kuma, kasashen Amurka da Koriya ta kudu su dakatar da atisayen sojan hadin gwiwar da suke yi nan da nan, ta yadda za su fita daga mawuyacin halin tsaro da suke ciki yanzu, da kuma kokarin ganin mayar da su kan teburin yin shawarwari. Sannan a lokacin da ake kokarin kawar da nukiliya daga yankin Koriya, dole ne a yi kokarin bullo da tsarin tabbatar da kwanciyar hankali a yankin, ta yadda za a warware batutuwan da suke kulawa a lokaci guda domin samun dabarar karshe ta kawo zaman lafiya har abada a yankin Koriya."

Dadin dadawa, game da makomar yin hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, Wang Yi ya jaddada cewa, duk da cewa tattalin arzikin kasashen duniya yana fuskantar sauye-sauye sosai, kasar Sin ba za ta rage yadda ta ke tallafawa kasashen Afirka.

Sannan, Wang Yi ya yi bayani game da manufar diflomasiyya mai sigar kasar Sin, inda ya nuna cewa, bai kamata a rarraba kasashe zuwa rukunin kasashe masu ba da jagoranci ko kasashen da ake jagorantarsu ba. Wang Yi ya bayyana cewa, "Ya kamata mu ce daukar nauyi maimakon kalmar jagoranci. Manyan kasashe sun fi kananan kasashe samun albarkatu da karfi. Ko shakka babu, ya kamata manyan kasashen duniya su dauki karin nauyi da kuma bayar da karin gudummawa. A matsayinta kasa mai kujerar dindindin a kwamitin sulhu na MDD, kasar Sin tana son sauke nauyin tabbatar da zaman lafiya da tsaro dake wuyanta. Kuma a matsayinta na kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya, kasar Sin tana son bayar da karin gudummawa wajen bunkasa tattalin arzikin duniya baki daya. Bugu da kari, a matsayinta na kasa mai tasowa mafi girma a duk duniya, kasar Sin tana son taka karin rawa wajen kare muradun dukkan kasashe masu tasowa."

Mr. Wang Yi ya bayyana cewa, yayin da kasar Sin ke karbar shugabancin karba-karba na kungiyar kasashen BRICS a bana, kasar Sin za ta shirya taron tattaunawa a tsakanin kasashe masu tasowa da kungiyoyin kasashe masu tasowa domin kokarin samun karin abokai ga kasashen BRICS. (Sanusi Chen, Maryam Yang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China