in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin: rahoton aikin gwamnati ya dora muhimmaci kan kyautata zaman rayuwar jama'a
2017-03-07 14:23:40 cri

Yayin da ake gudanar da taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, wakilai kimanin 3000 dake cikin majalisar suna kokarin tantance shirin aikin da gwamnatin kasar ta gabatar. Abokin aiki Bello Wang na dauke da karin bayani dangane da batun.

Rahoton aiki da firaministan kasar Sin Li Keqiang ya gabatar a madadin gwamnatin da yake jagoranta ya shafi abubuwa masu alaka da zaman rayuwar jama'a da yawa. Cikinsu wadanda suka fi janyo hankalin 'yan majalisun kasar sun hada da samar da karin guraben aikin yi, da saukaka fatara, da kokarin kyautata zaman rayuwar jama'a, da dai makamantansu.

Ga misali, a fannin samar da guraben aikin yi, gwamnatin Sin ta sanya buri na baiwa mutane fiye da miliyan 11 matsayin aiki a shekarar da muke ciki. Wannan buri ya zarce alkaluman da aka sanya a bara da karin guraben aikin yi miliyan 1. Duk da haka, firaminista Li ya bayyana a madadin gwamnatinsa cewa,

"Za a iya cimma wannan buri ne, ta la'akari da yanayin da tattalin arzikin kasarmu ke ciki, da yadda masana'antun kasar ke samar da karin ayyukan yi."

Sai dai a nata bangare, gwamnatin za ta dauki jerin matakai don tabbatar da ganin burin nan da ta sanya ya cika, matakan da suka hada da taimakawa kafa sabbin kamfanoni, da sai kaimi ga samar da karin ayyukan yi. A nasu bangare kuma, 'yan majalisun kasar Sin sun fahimci matsin lambar da gwamnati take fuskantar a fannin samar da ayyukan yi, duba da yadda yawan daliban jami'o'in da za su kammala karatu a wannan shekara zai kai miliyan 7 da dubu 950. Sai dai sun nuna goyon baya ga matakan da gwamantin ta dauka. A cewar Zhang Yunling, wani dan majalsiar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin, kuma shehun malami mai nazarin ilimin al'umma, matakan da gwamnatin ta dauka sun dace.

"Yanzu yanayin tattalin arzikin duniya na tabarbarewa, sa'an nan yadda ake daidaita tsarin masana'antu, da rufe wasu masu fasahohin koma baya daga cikinsu, dukkansu za su haddasa sallamar ma'aikata da yawa. Karkashin wannan yanayi ne, gwamnatinmu ta dora muhimmanci kan samar da ayyukan yi da rage talauci, hakan ya shaida yadda gwamnatinmu take kokarin sauke nauyin dake bisa wuyanta."

Har wa yau kuma, wani batu da 'yan majalisun kasar Sin suka fi mai da hankali a kai shi ne sashen ilimi. Don rage gibin dake tsakanin mazauna birane da kauyuka wajen samun damar shiga makarantu, da kara samar da daidaituwa tsakanin makatantu daban daban, gwamnatin kasar Sin za ta kara kokarin tallafawa wasu makarantun da ba su da ingancin muhalli, da malamai masu kwarewa, sa'an nan za ta sanya makarantu dake da kwarewa su bada hidima ga karin mutane.

Dangane da batun ilimi, Gulinur Memet, wata 'yar majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, kuma mataimakin shugaban makarantar horar da fasahohin masana'antu ta jihar Xinjiang, ta ce tsakanin yankunan yammaci da gabashin kasar Sin, har yanzu akwai gibi a fannin kirkire-kirkire, da amfani da fasahohin zamani wajen samar da kayayyaki, amma ana kokarin rage gibin dake tsakaninsu ta fuskar ilimi. A cewarta,

"Ya kamata a baiwa kowa damar amfana da makarantu da malamai masu inganci, maimakon a kebe su cikin wani yanki. Ta haka, duk wani yaro ko wata yarinya, tun da shekarun isa shiga makarantu, za a iya ba su ilimi bisa adalci da daidaito. Matakin na cikin abubuwan da rahoton aikin gwamnati ya ambata, a ganina ya dace da yanayin da muke ciki."

Ban da haka kuma, cikin rahoton gwamnatin kasar Sin, an bayyana matakin da za a dauka don taimakawa tsofaffin da suka bar gidajensu suke zaune tare da yaransu. An ce, za a hada bayanan da suka shafi inshorar lafiya na wurare daban daban. Ta haka, duk inda aka tafi, ba za a gamuwa da matsalar ganin likita, da amfani da ishorar lafiya ba.

Sauran manufofin da gwamnatin kasar Sin ta yi alkawarin dauka cikin rahotonta sun shafi rage talauci, da kiyaye muhalli, da dai makamantansu.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China