in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An duba rahoton aikin gwamnatin kasar Sin
2017-03-06 13:45:27 cri

A jiya Lahadi 5 ga watan nan ne aka kaddamar da taron shekara shekara, na majalisar wakilan kasar Sin na bana a nan birnin Beijing. Yayin taron, firayin ministan kasar Sin Li Keqiang ya gabatar da rahoton aikin gwamnatin kasar, inda ya yi nuni da cewa, kasar Sin tana kokarin cimma burin tabbatar da nufin karuwar GDP da kaso 6.5 bisa dari a shekarar bana da muke ciki, kana za a kara samar da guraben aikin yi sama da miliyan 11 a garuruwan kasar. Ban da haka kuma, za a kayyade adadin mutanen da suke rasa aikin yi zuwa kasa da kaso 4.5 bisa dari.

Masanan da abin ya shafa sun bayyana cewa, duk da cewa kasar Sin tana fuskantar matsaloli da dama a fannoni daban daban a bana, amma hasashen da aka yi ya dace da yanayin da kasar ke ciki.

Shehun malamin dake aiki a ofishin nazari da kuma ba da shawara kan harkokin kasa na majalisar gudanarwar kasar Sin Yao Jingyuan yana ganin cewa, hasashen da aka yi game da karuwar tattalin arzikin kasar Sin a bana, wato na samun kaso 6.5 bisa dari ya dace da manufar da aka tsara a kasar, wato kafa al'umma mai wadata a fadin kasar ta Sin. Hakan ya nuna niyyar da ake da ita, ta samun ci gaban tattalin arziki sannu a hankali, ta kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, da ta majalisar gudanarwar kasar Sin. Yao Jingyuan ya bayyana cewa, "Firayin ministan kasar Sin ya bayyana cewa, za a yi kokarin samun karuwar GDP da kaso 6.5 bisa dari a kasar Sin, hakan ya dace da manufar da aka tsara, wato tabbatar da al'umma mai wadata a fadin kasar. A cikin 'yan shekarun da suka gabata, kusan ko wace shekara, karuwar GDP a kasar Sin na kaiwa kaso 6.5 bisa dari. A saboda haka, wannan manufa ta dace da hakikanin yanayin da kasar Sin ke ciki. A halin da ake ciki yanzu, ko da yake kasar Sin ta samu babban sakamako wajen ci gaban tattalin arzikin ta, amma a sa'i daya kuma tana fuskantar matsaloli da kalubale da dama a fannoni daban daban. A cikin shekarar bana da muke ciki, aiki mafi muhimmanci shi ne gudanar da kwaskwarima kan tsarin tattalin arziki, musamman ma wajen tsarin samar da kayayyaki. Kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, da majalisar gudanarwar kasar Sin suna sa ran za a cimma burin tabbatar da manufar samun ci gaban tattalin arziki sannu a hankali, ta hanyar yin kirkire kirkire, da samun moriyar juna ba tare da rufa rufa ba, da haka tattalin arzikin kasar Sin zai shiga wani sabon matsayi."

Game da manufar da aka gabatar a cikin rahoton aikin gwamnatin, wato ta kara samar da guraben aikin yi sama da miliyan 11 a garuruwan kasar, mataimakin shugaban sashen nazarin kudaden kasashen duniya, na jami'ar Renmin ta kasar Sin Xiang Songzuo yana ganin cewa, samar da guraben aikin yi a kasar Sin ya shafi tsarin tattalin arzikin kasar. ya ce idan ana son kyautata wannan aiki, wajibi ne a yi kwaskwarima domin kyautata tsarin tattalin arziki. Ya ce yanzu haka kasar Sin kamata ya yi ta kara gudanar da kirkire kirkire a wasu sana'o'i. Misali, a wasu yankunan dake kudancin kasar, wasu kamfanoni suna amfani da na'urori masu sarrafa kan su maimaikon mutane. Kana a ko wace shekara, daliban da yawansu ya kai miliyan bakwai ko takwas, suna kammala karatu a jami'o'i, wadanda kuma ke bukatar neman aikin yi, amma abu ne mai wuya su samu aikin da suke so. Ban da haka kuma, wasu mutane suna rasa aikin yi daga kamfanoni. To don haka, idan ana son warware duk wadannan matsaloli, ya fi dacewa a dauki matakai na kyautata tsarin tattalin arzikin kasar.

Firayin minista Li Keqiang ya bayyana cewa, makasudin samun ci gaban tattalin arziki shi ne, samar da guraben aikin yi ga al'ummar kasar, tare kuma da samar da wadata gare su. A bana, gwamnatin kasar Sin za ta kara mai da hankali kan samar da guraben aiki. An kuma yi hasashe cewa, adadin guraben aikin yi da za a samar a bana, zai zarta na bara da miliyan 1.

Kasar Sin babbar kasa ce ta cinikayya, tana kuma samun ci gaban tattalin arziki ne ta hanyar gudanar da cinikin waje, da zuba jari, da kuma kashe kudade. A cikin rahoton aiki na bana, an bayyana cewa, ana gudanar da cinikin waje lami lafiya a kasar Sin, kuma ba a yi hasashe kan batun ba, shehun malamin dake aiki a ofishin nazari da kuma ba da shawara kan harkokin kasa na majalisar gudanarwar kasar Sin Yao Jingyuan yana ganin cewa, hakan ya alamanta cewa, kasar Sin tana kara mai da hankali kan ingancin cinikin waje, yana mai cewa, "A shekarar 2015, adadin hada hadar shige da fice a kasar Sin ya ragu da kaso 7 bisa dari. A bara kuma, adadin ya ragu da kaso 0.9 bisa dari, yayin da a bana kuma wata kila adadin ya karu."

Kazalika, gwamnatin kasar Sin tana kara ba da muhimmanci kan farashin kayayyaki a kasar, inda ake fatan shawo kan karuwar yawan farashin kayayyakin da jama'a suke saya wato CPI da kaso 3 bisa dari. Wakilin taron majalisar wakilan kasar Sin Gong Shuguang ya bayyana cewa, kasar Sin za ta cimma wannan buri, yana mai cewa, "Kowace shekara, muna fuskantar matsaloli iri daban daban, amma har kullum muna warware su. Shi ya sa ya dace mu ci gaba da yin kokari matuka a nan gaba."

A cikin rahoton aikin, firayin minista Li Keqiang shi ma ya gabatar da muhimman ayyukan gwamnatinsa a fannoni tara a bana, kana daukacin shugabannin sassan gwamnatin sun bayyana cewa, za su kara zurfafa kwaskwarima a fannoninsu, domin sa kaimi kan ci gaban tattalin arzikin kasar Sin.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China