in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a kaddamar da taron CPPCC na bana a Beijing
2017-03-03 12:32:56 cri

A yau Jumma'a 3 ga wata da yamma, agogon kasar Sin, za a kaddamar da taron shekara shekara na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin CPPCC na bana a babban dakin taron jama'a dake nan birnin Beijing, hakan ya alamanta cewa, za a fara gudanar da taruka biyu na kasar Sin wato taron majalisar wakilan kasar da taron majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar, wadanda ke jawo hankalin jama'a a hukumance. A yammacin jiya Alhamis ne, majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin ta kira taron manema labarai, inda kakakin watsa labarai na taron majalisar Wang Guoqing ya bayyana a lokacin da ya ke amsa tambayoyin manema labarai cewa, yanzu tattalin arzikin kasar Sin yana samun ci gaba yadda ya kamata, kuma zai ci gaba da taka muhimmiyar rawa ga ci gaban tattalin arzikin duniya.

Yayin taron manema labaran da aka gudanar a jiya, kakakin babban taron majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin na bana Wang Guoqing ya bayyana cewa, a sabuwar shekarar da muke ciki, kasar Sin za ta ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen ga ci gaban tattalin arzikin duniya, kana ya bayyana cewa, kasar Sin tana kiyaye 'yancin kasashen duniya na yin zirga-zirga a tekun kuduncin kasar Sin kamar yadda ta tanada.

A yayin taron na jiya, manema labarai na kasar Sin da na kasashen waje sun yi ta gabatar da tambayoyin dake shafar ci gaban tattalin arzikin kasar Sin, kakaki Wang Guoqing ya yi musu cikakken bayani har ma da alkaluma, ya ce, a halin da ake ciki yanzu, duk da cewa tattalin arzikin duniya bai samu farfadowa yadda ya kamata ba, amma adadin GDP na shekarar 2016 na kasar Sin ya zarta yuan biliyan dubu 70, adadin da ya karu da kaso 6.7 bisa dari idan aka kwatanta da na shekarar 2015, kuma karuwarsa ta kasance a sahun gaba a fadin duniya. Kana kasar Sin ita ce kasa ta biyu mafi samun saurin ci gaban tattali arziki a fadin duniya, a saboda haka, a shekarar bara wato 2016, kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa wajen ga ci gaban tattalin arzikin duniya, wadda ta kai kaso 33.2 bisa dari, dalilin da ya sa haka shi ne domin karuwar tattalin arzikin kasar Sin ta samar da bukatun kasuwanni ga tattalin arzikin duniya, haka kuma ta jawo karin jarin da aka zuba, tare kuma da samar da karin kayayyakin da ake bukata, da karin damammakin hadin gwiwa dake tsakanin kasa da kasa. Game da yanayin da tattalin arzikin kasar Sin ke ciki a bana, kakaki Wang Guoqing ya bayyana cewa, "A halin da ake ciki yanzu, tattalin arzikin kasar Sin yana samun ci gaba yadda ya kamata, amma duk da haka, za mu ci gaba da yin kokari. Bisa hasashen da masana tattalin arzikin kasar Sin suka yi kan yanayin tattalin arzikin da kasar Sin ke ciki a yayin taron da aka gudanar a watan Janairun bana, ya nuna cewa, tattalin arzikin kasar Sin yana ci gaba da samun karuwa kamar yadda yake a cikin 'yan shekarun da suka gabata, yanzu haka ana gudanar da kwaskwarima kan tsarin tattalin arzikin kasar, wannan ya sa aka yi hasashe cewa, tattalin arzikin kasar Sin zai kara samun ci gaba, a sa'i daya kuma, zai ci gaba da taimakawa bunkasuwar tattalin arzikin duniya."

Kazalika, game da shakkun da ake nunawa kan matakan kwaskwarimar kasar Sin, kakaki Wang Guoqing ya bayyana cewa, kasar Sin za ta ci gaba da kara zurfafa kwaskwari a kasar, ba zai yiyu ta kammala aikin ba. Yana mai cewa, "Watakila kun tarar da cewa, a farkon watan Fabrairun bana, a yayin taro na 32 na kungiyar kula da aikin zurfafa kwaskwairma daga duk fannoni a fadin kasar Sin, ta jaddada cewa, za a kara mai da hankali kan aikin kwaskwarima a nan gaba, kuma an bukace mu mu kara kokari matuka, saboda haka, ba zai yiwu a kammala wannan aikin a cikin kasar Sin ba."

Game da rahoton da manema labarai na kasar Amurka suka gabatar wai kasar Sin ta gina kayayyakin soja a tsibiran tekun kudancin kasar, wanda hakan zai kawo barazana ga harkokin sufuri a yankin, Wang Guoqing ya yi nuni da cewa, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin da na ma'aikatar tsaron kasar Sin sun sha yin bayyani kan wannan batun, shi ya sa kamata ya yi a kara tabbatar da cewa, tsibiran dake tekun kudancin Sin, yankin kasar Sin ne, don haka kasar Sin ta yi gine-gine a yankinta, wannan 'yancin ne na kasa mai cin gashin kan ta, kuma dokar kasa da kasa ta amince da haka ne, Wang Guoqing ya ce, "An ce, kasar Sin ta kawo barazana ga zirga-zirgar sauran kasashe a tekun kudancin Sin, hakan bai dace ba, gwamnatin kasar Sin ta fi mai da hankali wajen ganin an gudanar da zirga-zirga cikin kwanciyar hankali a yankin, saboda kasar Sin kasa ce mafi girma da kuma fadin kasa a yankin, kuma har kullum kasar Sin tana kiyaye 'yancin sufuri na kasashen duniya kamar yadda dokar kasa da kasa ta fayyace, kana kasar Sin ta riga ta kafa wani tsarin hadin gwiwa tsakaninta da wasu kasashe domin tabbatar da kwanciyar hankalin sufuri a yankin."

Ban da haka kuma Wang Guoqing shi ma ya yi bayani dalla-dalla kan sakamakon da aka samu wajen aiwatar da shirin "ziri daya da hanya daya", inda ya bayyana cewa, kawo yanzu kasar Sin tana gudanar da hadin gwiwa da kasashe 20 da wannan shirin ya shafa.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China