in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron majalisar CPPCC a kasar Sin
2017-03-03 19:00:47 cri

A yau Jumma'a ne aka bude taro na 5 na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin CPPCC ta 12, a nan birnin Beijing.

Da karfe 3 na yammacin wannan rana ne aka kaddamar da taron majalisar CPPCC, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping, da sauran manyan kusoshin kasar suka kasance cikin mahalartar taron, suka kuma saurari rahoton aiki da shugaban majalisar CPPCC Yu Zhengsheng ya gabatar, a madadin zaunanen kwamitin majalisar.

Daga kuma wannan lokaci zuwa fiye da kwanaki 10 masu zuwa, 'yan majalisar sama da 2100, wadanda suke wakiltar jam'iyyun siyasa, da al'ummomin kasar daban daban, da sana'o'i iri-iri, za su gabatar da shawarwari game da manufofin kasar Sin, musamman ma ta bangaren gyare-gyare da neman ci gaba.

Kasancewar bana shekara ce mai muhimmanci a kokarin aiwatar da shirin kasar Sin na raya kasa cikin shekaru 5, kuma wani lokaci ne da ake kokarin daidaita tsarin samar da kayayyaki a kasar, hakan ya sa shugaban majalisar ta CPPCC Yu Zhengsheng, ya bukaci 'yan majalisar da su mai da hankali kan batun tattalin arziki. A cewarsa,"Ya kamata mu lura da yanayin da tattalin arzikin kasarmu ke ciki, a kira taruka na musamman, domin tattauna batun daidaita tsarin samar da kayayyaki, da kyautata huldar dake tsakanin gwamnati da 'yan kasuwa. Haka kuma za mu gabatar da shawarwari kan harkokin da suka shafi daidaita tsarin masana'antu, da farashin gidaje, da kasuwanci ta kwamfuta, da jigilar abinci, da dai makamantansu."

Har ila yau, Yu ya kara da cewa, 'yan majalisar CPPCC za su kara musayar ra'ayi, tare da wakilan yankunan Hongkong, Macau da Taiwan na kasar Sin, musamman ma kan bikin murnar cika shekaru 20 da dawowar yankin Hongkong cikin kasar Sin.

Ban da haka kuma, wani abin lura shi ne, cikin rahoton aikin da mista Yu ya gabatar, an jaddada rawar da majalisar take takawa a fannin sa ido kan gudanar da ayyukan gwamnati. An ce, aikin sa ido na majalisar CPPCC ya kasance daya daga cikin bangarorin tsarin sa ido irin na gurguzu na kasar Sin. Ya ce,"Ana gudanar da aikin sa ido ne bisa tushen tsayawa kan zama karkashin jagorancin jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, da turbar gurguzu irin ta musamman na kasar Sin. Sa'an nan 'yan majalisar CPPCC na jam'iyyu da kabilu daban daban, za su iya ba da shawarwari ko kuma yin suka kan aikin gwamntin kasar, bisa kundin tsarin majalisarmu."

Bayan haka, Yu Zhengsheng, ya kara nanata cewa, yayin da 'yan majalisar suke kula da aikin sanya ido kan harkokin gwamnati, ya kamata su yi kokarin fadin albarkacin bakinsu, gami da fadin gasikiya. A cewarsa,

"Ya kamata a yi suka ga mutumin da ya yi kuskure kan kuskurensa kawai, sa'an nan bai kamata a yi karyar da za ta dorawa wani laifin da bai aikata ba. Mu fadi albarkacin bakinmu, tare da fadin gaskiya. Wani lokaci a kan samu bambancin ra'ayi, amma ya dace mu girmama ra'ayin da sauran mutane suke fada, ko da suka ne maras dadi. Ta haka, za mu iya samar da wani muhalli, inda kowa zai iya fadin duk wani abun da ke zuciyarsa, kuma zai fadi hakan bisa doka. "

Shugaban Yu Zhengsheng ya kara da cewa, a wannan shekarar da muke ciki, majalisar CPPCC za ta dora cikakken muhimmanci, kan manyan ayyukan jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin da na gwamnatin kasar, sa'an nan ta sanya ido kan yadda suke gudanar da ayyukansu. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China