in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nijeriya ta tsaurara matakan tinkarar Ebola
2014-08-12 17:31:56 cri


Baya ga kasashen Guinea da Liberia da Saliyo, Nijeriya ta zama kasa ta hudu a nahiyar Afirka da aka gano bullar cutar Ebola, inda ya zuwa ranar 11 ga wata aka tabbatar da mutane 10 da suka kamu da cutar. Abokiyar aikinmu Lubabatu na dauke da karin bayani.

Ya zuwa ranar 11 ga wata, an gano mutane 10 da suka kamu da cutar Ebola a tarayyar Nijeriya, kuma dukkansu a jihar Lagos. An ce daga cikin mutanen, biyu sun mutu, ciki hadda mutumi da ya shigar da cutar daga kasar Liberiya, dayar kuma nas ce da ta yi jiyyarsa. Ban da su, akwai wasu mutane 177 da aka killace, abin da ya nuna cewa, kasar Nijeriya na fuskantar wani babban kalubale.

Kafin wannan, a ranar 8 ga wata, shugaban Nijeriya, Goodluck Jonathan ya fitar da sanarwa, inda ya sanar da kafa dokar ta baci a duk fadin kasar, tare da ware naira biliyan 1 da miliyan 900 domin dakile yaduwar cutar ta Ebola. Sanarwar ta kuma bukaci makarantu a matakai daban daban da su tsawaita lokacin hutu ga dalibai, tare da yin kira ga 'yan kasar da su kaurace wa sauraron jita-jita da kuma kauracewa wuraren da mutane ke taruwa. Baya ga haka, shugaban ya kuma yi kira ga 'yan kasar da kada su yi jigilar gawawwaki daga kasashen waje.

A halin yanzu, sassan kiwon lafiya na jihohi na hada gwiwa da gwamnatin tarayya da kananan hukumomi wajen fadakar da al'umma game da hanyoyin kandagarkin cutar Ebola, kuma sun gabatar da matakai da dama. Ministan kiwon lafiya na kasar ya yi kira ga al'umma da su rika wanke hannayensu da kula da tsabta, kuma su rika dagawa juna hannu in suna son gaisawa maimakon rungumar juna da yin musafaha. A Abuja, hukumar kiwon lafiya ta fassara bayanai game da cutar Ebola zuwa harsunan Hausa da Yarbanci da Igbo, don watsa su ta rediyo da talabijin da jarida da kuma yanar gizo. Ban da haka, kungiyoyin musulunci da kirista a kasar sun bayar da sanarwa, inda suka yi kira ga mabiyansu da su kauracewa tarurruka. Ban da haka, kananan hukumomi a kasar ma sun bukaci asibitoci da su kebe dakunan da za a killace masu cutar, tare da bukatar likitoci da nas-nas da su yi shirin ko ta kwana don tinkarar cutar.

Duk da haka, a wajen shawo kan yaduwar cutar, Nijeriya na fuskantar matsaloli da dama. Na farko, jita-jita na karbuwa a tsakanin al'umma sakamakon rashin sani. A kwanakin nan, akwai jita-jitar da ke cewa, yin wanka da ruwan gishiri na iya taimaka wajen rigakafin cutar, abin da a cewar ministan kiwon lafiya jita-jita ce da ko kadan ba ta da tushe, kuma yana fatan al'umma za su amince da bayanan gwamnati da na kimiyya. Duk da haka, a labaran da kafofin yada labarai na kasar suka bayar, an ce, har yanzu akwai mutane da ke amincewa da yin amfani da ruwan gishiri wajen rigakafin cutar. Har ila yau, ko da yake dukkan mutanen da aka gano sun kamu ko ake da shakku game da kamuwa da cutar ta Ebola suna birnin Lagos ne, a hannu guda akwai jita-jitar da ke cewa an fara samun bullar cutar a Abuja, har ma a kan alakanta mutanen da suka mutu sakamakon wasu cututtuka na yau da kullum da cutar ta Ebola, lamarin da ya tada tashin hankalin al'umma.

Ban da jita-jita, rashin samun likitoci ma wata babbar matsala ce da ake fuskanta. Inda tun daga ranar 1 ga watan Yulin da ya gabata, likitocin asibitoci mallakar gwamnati ke fara yajin aiki a kasar baki daya, kuma har zuwa lokacin bullar cutar a kasar, kungiyar likitocin kasar ta tsai da kudurin dakatar da yajin aiki. Ba a tabbatar ko likitocin za su koma aiki ba ko a'a. A jihar Lagos ma mahukunta sun amince da rashin likitoci a matsayin matsalar da ake fuskanta, kuma suna fatan masu aikin sa kai za su iya taimaka wa gwamnati wajen tinkarar cutar Ebola. Domin ba wa likitoci kwarin gwiwar sa hannun wajen tinkarar cutar, gwamnati ta kuma alkawarta samar musu inshorar lafiya. A cewar babban sakataren kungiyar Red Cross ta kasar, ya zuwa yanzu akwai masu aikin sa kai 18 da suka shiga aikin shawo kan cutar Ebola a Lagos, wadanda kuma suke kula da aikin bin diddigin wadanda suka taba haduwa da masu cutar da sa ido a kan mutanen da ake shakkar ko sun kamu da cutar da kuma fadakar da al'umma game da kandagarkin cutar, a yayin da ake ci gaba da fama da karancin likitoci da masu hada magunguna da nas-nas da ake bukata.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China