in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya kamata a yi taka tsantsan a kan Ebola, in ji WHO
2014-04-09 16:48:16 cri

A ranar 8 ga wata, hukumar kiwon lafiya ta duniya(WHO) da ke da hedkwatarta a birnin Geneva ta bayyana cewa, cutar Ebola da ake fama da ita a yanzu haka a yammacin Afirka na daya daga cikin cututtukan da suka fi kawo kalubale tun lokacin da aka fara gano ta, abin da ya kamata a yi taka tsantsan a kai.

An fara gano cutar ne a kasar Guinea a karshen watan Maris na wannan shekara. Alkaluman da hukumar WHO ta fitar a ranar 8 ga wata sun shaida cewa, cutar ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 101 a kasar Guinea, tare da wasu 10 a Liberia. A wannan rana, mataimakin babban darektan hukumar WHO da ke kula da harkokin kiwon lafiya da muhalli, Keiji Fukuda ya bayyana wa manema labarai cewa, annobar Ebola da ke addabar yammacin Afirka na daya daga cikin cututtukan da suka fi kawo kalubale, ya ce, "Me ya sa muka ce annobar da ake fama da ita yanzu na daya daga cikin cututtukan da suka fi kawo kalubale? Na farko, an gano cutar ne a sassa daban daban maimakon wuri daya, ciki har da Conakry, babban birnin kasar Guinea. Na biyu, ba a taba gano cutar a wannan shiyya ta Afirka ba, don haka, jama'a ba su da kwarewa wajen shawo kanta. Na uku, a yayin da aka gano cutar a wasu sassa da dama, jita-jita ma na yaduwa, abin da ya sa muke ta samar da labaran da suka shafi annobar, don neman ganin an sassauta yaduwarta."

Stephane Hugonnet, masani a hukumar WHO, ya yi nuni da cewa, a kasashen Guinea da Liberia ne kawai aka gano cutar Ebola, kuma a Saliyo da Ghana da kuma Mali da ake jita-jitar cewa an gano cutar, har yanzu ana bincike kan mutanen da suka nuna alamun kamuwa da ita, amma babu tabbas. Ya ce, abin da ya kamata a yi yanzu shi ne a sa ido sosai a kan yaduwar cutar da kuma sassan da aka gano bullarta, ya ce, "A zahiri dai, an gano annobar a kasashe biyu, don haka, ya yiwu za a kara gano cutar a sauran wasu kasashe, abin da ya sa dole mu yi taka tsantsan a kan lamarin."

A shekarar 1976, karo na farko ne aka gano cutar Ebola a kasar Sudan da jamhuriyar dimokuradiyyar Congo, cutar da kan yi barna sosai da zarar ta kama mutum. Barkewar wannan annobar a shekarar 2000 a Uganda ta fi kazanta, domin kuwa ta hallaka mutane har 224. A cewar Keiji Fukuda, Ebola cuta ce mai barna sosai, kuma za a kara gano mutanen da suka kamu da ita nan da watanni masu zuwa. Duk da haka, ya bayyana cewa, in an dauki matakan kariya da suka dace, yawan mutanen da suke kamuwa da cutar zai ragu kwarai, ya ce, "Za a iya shawo kan cutar Ebola. Mun san yadda cutar ke yaduwa, kuma mun san matakan da ya kamata a dauka don hana yaduwarta, in dai an dauki matakan da suka dace, za a iya sassauta yaduwar cutar."

Fukuda ya kara da cewa, hukumar WHO za ta samar da taimako ga kasashen da aka gano annobar, kuma za ta dauki matakan da za su hana yaduwar cutar tare da samar da jiyya mai inganci ga masu fama da cutar. Ban da haka, hukumar za ta kara tuntubar al'ummar yankin, don sassauta damuwarsu dangane da hakan.

A ganin hukumar WHO, lokaci bai yi ba da a sanya haramcin tafiye-tafiye ko na cinikayya kan kasashen da cutar ta bulla.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China