in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na kokarin tallafawa kasashe uku na yammacin Afirka wajen yaki da cutar Ebola
2014-08-11 17:07:56 cri

Hukumar kula da kiwon lafiya ta duniya wato WHO, ta bayar da sanarwa a ranar 8 ga wata a birnin Geneva, cewa yaduwar cutar Ebola ta zama wani lamarin kiwon lafiya na gaggawa dake jawo hankulan kasashen duniya. Ka na ta yi kira ga kasashen duniya da su ba da taimako ga kasashen yammacin Afirka dake fama da wannan cuta. Har wa yau a dai wannan rana, gwamnatin kasar Sin ta tashi wani jirgin sama mai dauke da kayayyakin aikin jinya har Ton sama da 80, wanda a yanzu haka ke kan hanyar sa zuwa kasashen da cutar ta fi shafa.

A wannan duniyar da muke ciki, tabbas ana iya samun sauki wajen gudanar da harkoki rayuwa a fannoni daban daban, ta hanyar yin cudanyar juna, a sa'i guda kuma, akwai bukatar a fuskanci kalubale tare.

Yayin da wannan cutar ta Ebola ke kara tsanani, kuma da yake ba safai a kan gamu irin ta ba, ya sa ake bukatar hadin kai wajen tinkarar ta cikin gaggawa. Nauyin da kuma ya rataya a wuyan kasashen duniya baki daya.

Ana dai ganin a matsayin ta na muhimmiyar kasa a duniya, kamata ya yi kasar Sin ta dauki wani nauyi game da wannan aiki mai muhimmnaci.

Manazarta dai na ganin kasashen dake yammacin Afirka masu fama da yaduwar wannan cuta ta Ebola, ba su da wani cikakken tsarin kiwon lafiyar jama'a, kasancewar wasun su ba su dade da kawar da rikice-rikice dake da suka auka musu ba cikin lokaci mai tsaho. Matakin da ya kasance daya daga dalilan saurin yaduwar cutar ta Ebola.

A bayan da gwamnatin kasar Sin ta samar da kayayyakin shawo kan cutar na RMB miliyan daya ga kasashen Guinee, da Liberia, da Saliyo da kuma Guinee-Bissau kowace cikin watan Aflilu, a kuma ranar 7 ga watan nan, gwamnatin kasar ta bayar da sanarwar kara samar da kayayyakin taimako na jin kai, da darajar su ta kai RMB miliyan 30, ga kasashe uku daga cikin kasashen da aka samu bullar cutar.

Kasancewar kayayyakin da Sin ta samar abubuwa ne da wadannan kasashe ke bukata cikin gaggawa, an tabbatar da cewa za a isar da su zuwa ga kasashen dake matukar bukatar su ba tare da wani bata lokaci ba.

Bayan haka kuma, kungiyoyin kwararru a fannin kiwon lafiyar jama'a da kasar Sin ta aike zuwa kasashen Guinee, da Liberia da Saliyo, sun riga sun tashi tsakanin ranekun 10 da 11 ga watan nan. Kuma muhimman ayyuka da za su gudanar a kasashen uku su ne, taimaka wa ofisoshin jakadan kasar Sin dake wuraren wajen rarraba kayayyakin taimako, da horar da kwararrun wuraren wajen amfani da kayayyakin taimako yadda ya kamata, da kuma ba da jagoranci ga kungiyoyin aikin jinya na kasar Sin dake kasashen wajen yin kandagarkin yaduwar cutar da dai sauransu.

Game da wadancan kungiyoyin aikin jinya na kasar Sin, da suke kasashen uku kuwa, har yanzu suna ci gaba da ayyukansu a wannan yanayin da ake ciki na yaduwar cutar ta Ebola.

Kungiyar aikin jinya ta kasar Sin dake kasar Guinea tana aiki a asibitin sada zumunci tsakanin Sin da Guinea, wanda ya karbi mutum na farko da ya kamu da cutar ta Ebola a hedkwatar kasar. Ko da yake likitoci da masu ba da jinya guda 9 a asibitin sun kamu da cutar, har ma 6 daga cikinsu sun rasa rayukansu, amma duk da hakan ma'aikatan tawagar aikin jinyar kasar Sin, ba su taba dakatar da ayyukan da suke gudanarwa ba.

A kasar Liberia ma, asibitin babban birnin kasar ya dakatar da aiki na dan lokaci, kuma dukkan likitocin kasashen Masar da na Amurka, sun riga sun janye jikin su, amma a wannan yanayi mai tsanani da ake ciki, tawagar ma'aikatan jinya ta kasar Sin tana ta ci gaba da kasancewa a wani wuri dake kusa da Asibitin, inda kuma idan aka samu jiyyar gaggawa za su iya bada tallafi nan take.

Shugaban kungiyar aikin jinya ta kasar Sin dake kasar Saliyo, Wang Yaoping ya ce, yanzu haka tawagar sa na ci gaba da ayyukan ta kamar kullum, suna kuma zuwa asibiti a ko wace rana.

Sa'an nan al'amari ne dai cewa kasar Sin, ta riga ta jure babbar jarrabawa daga yaduwar tarin fuka na SARS, zuwa cutar murar tsuntsaye ta H7N9, hakan ya sa ta tattara fasahohi masu yawa, game da tinkarar lamuran gaggawa game da kiwon lafiyar jama'a.

Game da wannan cutar ta Ebola, a yayin da kasar Sin ke kokarin hana shigowar ta gida, a sa'i daya kuma tana fatan yadawa sauran kasashen waje fasahohin da ta samu na yaki da cututtuka.

Game da hakan, mai bada taimako ga babban daraktan hukumar WHO, Keiji Fukuda ya ce kasar Sin ta zuba jari da yawa a fannin kiwon lafiyar jama'a, ta kuma samu sakamako mai kyau game da jarin da ta zuba a fannin sa ido kan cututtuka, da samar da bayyanai da dai sauransu. Wannan dalili ne ya sa ta kai ga cimma nasara, da amsa muhimman batutuwa cikin lokaci, a yayin da take yaki da cutar murar tsuntsaye ta H7N9. Wanda hakan ya sanya fasahohin ta kasancewa masu amfani, ga dukkanin sassan duniya baki daya. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China