in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Matsalolin da ake fuskanta wajen shawo kan cutar Ebola
2014-08-04 17:22:18 cri



Cutar Ebola da ake fama da ita a yanzu haka a yammacin Afirka ya ta jawo hankalin duniya baki daya. Ahakika, ann fara gano cutar ne ce tuni a shekarar 1976, amma me ya sa a cikin tsawon kusan shekaru 40 da suka wuce, babu wata hanyar da aka gano ta shawo kan cutar, shin wadanne wahalhalu matsaloli ne ake fuskanta wajen tunkarar wannan cuta? Abokiyar aikinmu Lubabatu na tare da karin bayani.

An fara gano cutar Ebola ne ce tuni a shekarar 1979, amma a cikin tsawon shekaru 40 da suka wuce, babu wata hanyar da aka gano ta shawo kan cutar. A game da abinSakamakon da ya kawo wannan mawuyacin halin da ake ciki yanzu, dole sai mu yi nazari a kangame da wannan cutar.

Da farko, mun san cewa renon cutar Ebola na da wuya a cikin dakin gwaji. Dole ne a gudanar da gwajin da ya game da shafi cutar a cikin dakin gwajin da ke da matakan kariya masu inganci, amma dakunan gwaji da suka dace a yanzu haka kalilan ne a duniya baki daya.

Sa'an nan, Ebola cuta ce da ba safai ake ganinta ba, wadda kuma a kan gano same ta ne a yammacin Afirka kawai, har ma akwai mutane da dama da ba su taba jin sunan cutar ba, don haka ne, babu da wuya za a iya matsawa sosai ga masu nazari wajen binciken hanyar shawo kan cutar.

Har wa yau, ba kamar wasu cututtuka da su kan yadu a wani takamaiman lokaci cikin shekara ba, cutar Ebola ta kan barke ne ba zata, don haka, da wuya a yi hasashen aukuwarta da kuma yin rigakafinta.

Cutar Ebola da ake fama da ita yanzu haka a kasashen Guinea da Liberia da kuma Saliyo ya zama mafi tsanani da ake aka taba fuskanta, kuma ya zuwa yanzu akwai mutane fiye da 1000 da suka kamu da cutar ko kuma suka nuna alamar kamuwa da ita, a yayin da a baya baya nan, wasu mutane kalilan me ne kan kamu da cutar.

Ban da haka, rashin cin samun riba ma ya zama daya daga cikin dalilan da suka sa ba a fitar da magani ko allurar rigakafin cutar da sauri ba. Ana bukatar makudan kudade wajen nazarin magunguna da allurar rigakafin Ebola, a yayin da maganin ko allurar da ake bukata ba su da yawa a halin yanzu, don haka, babu wata masana'anta mai zaman kanta da take son zuba jari kan binciken wannan cutan. Kamar yadda Ben Neuman, manazarcin ilmin cututtuka a jami'ar Reading ta Birtaniya yta fada, "babu wani kamfanin samar da magungunan da zai so ya yi nazari kan cutar Ebola in ya yi la'akari da ribar da zai iya cisamu."

A halin yanzu, gwamnatoci nan Amurka da sauran wasu kasashe masu sukuni ne ke ba da kudin gudanar da wannan nazari, wadanda suka ba da kudin ne ba sabo da gano hanyar warkar da masu fama da cutar ba, amma don magance harin da ake iya kaiwa ta yin amfani da cutar.

A cikin irin wannan yanayi ne, ba a samu saurin ci gaba wajen nazarin maganin shawo kan cutar ba, sai ya zuwa lokacin barkewar cutar a wannan karo, aka fara gaggauta nazarin.

A fadin duniya, yawancin magunguna ko alluran rigakafin Ebola da ake nazari a kansu suna can kasar Amurka ne, sai amma dai babu daya daga cikinsu da aka yi gwajinsu a jikin dan Adam. A labarin da aka bayar, an ce, a gwajin da aka yi a jikin birai, wani maganin da rundunar sojan kasar Amurka ta samar da kudin nazarinsa ya fara ba da yin amfani,tasiri kuma Fred Hayden, wani masanin ilmin cututtuka masu yaduwa a jami'ar Virginia ya ce, "ya yiwu maganin zai ya taimaka, bisa ga gwajin da aka yi a jikin dabbobi, amma dole ne a gudanar da gwajin a jikin dan Adam, in ba haka ba, ba wanda ya sani ko maganin zai yi aiki ko a'a."

A halin da ake ciki yanzu, abin da likitoci ke iya yi shi ne su taimaka wa masu fama da cutar sassauta zazzabinsu da amai da zawo da suke fuskanta. Duk da cewa, Ebola cuta ce muguwamai saurin halaka jama'a, amma in wanda ya kamu da cutar ya je wurin likita cikin sauri zai iya samun damar warkawawarkewa.

Amma ko ana iya yin amfani da magunguna ko alluran rigakafi da ba a gudanar da gwajinsu gwada su a jikin dan Adam ba a sassan yammacin Afirka da cutar ke barna? A game da haka, ana fama da sabanin ra'ayi sosaAkwai sabanin ra'ayoyi sosai game da wannan batui. A ganin Peter Piot, masani a kwalejin nazarin harkokin kiwon lafiya da cututtukan da a kan gano ake fama da su a yankuna masu zafi da ke jami'ar London ya ce, sakamakon mummunan halin da ake ciki yanzu, ya kamata a yi tunani a kan yin amfani da magungunan da alluran. Duk da haka, akwai masana da dama da suke tare da ra'ayin cewa, bai dace ba a yi amfani da magani da alluran da ba a gudanar da gwajinsu gwada su a jikin dan adam ba, sabo da hakan na iya haddasa babbar masifabarna.

Gregory Hartl, kakakin a hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO ma ya ce, a halin da ake ciki yanzu, hukumarsa ba ta da shirin samar da magungunan da ake gwajinsu ko kuma gudanar daaiwatar da gwajin a yankunan da ke fama da cutar a yammacin Afirka.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China