in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bai kamata Sinawa su damu da cutar Ebola ba, in ji kakakin WHO
2014-07-31 16:37:58 cri

Kakakin hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO Paul Garwood ya bayyana a ranar talata 30 ga wata cewa, ko da yake wadansu kasashe a nahiyar Afrika na fama da cutar Ebola, bai kamata Sinawa su damu game da hakan ba saboda ganin wata 'yar yankin Hongkong ta kamu da cutar bayan data dawo daga nahiyar Afirka.

An ba da labari cewa, wata 'yar yankin Hongkong da ta dawo nan kasar Sin daga Kenya ta nuna alamar kamuwa da cutar Ebola, abin da ya jawo hankalin mutane da dama. A wannan rana da dare, kafar yada labarun wurin ta ba da labari cewa, binciken da aka yi ya shaida cewa, wannan mata ba ta kamu da cutar ba.

Kakakin hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO Paul Garwood ya nuna cewa, ya kamata kasashe daban-daban su kara mai da hankali kan sa ido da yin rigakafin cutar Ebola, idan masu yawon shakatawa suna zazzabi, amai, da rashin karfin jiki ko ciwon jiki a cikin makonni uku da dawowan su daga nahiyar Afrika, ya kamata a yi taka tsantsan da neman taimako daga hukumar kiwon lafiya nan da nan. Ya zuwa yanzu dai, WHO ba ta gabatar da kudurin hana yawon shakatawa ko yin ciniki da kasahen Afrika dake fama da wannan cuta ba, a cewarta, saboda babu mataki mai amfani wajen warkar da cutar da allurar yin rigakafi, ya kamata a inganta ayyukan yin rigakafi.

A wani bangaren kuma kasar Afrika ta kudu ta dauki damara kan wannan cuta. Hukumar kiwon lafiya ta kasar ta sanar da daukar shirin ko ta kwana a ran 30 ga wata, domin hana yaduwar cutar zuwa iyakarta. Ministan kiwon lafiya Aaron Motsoaledi ya ce, ya kamata Afrika ta kudu ta dauki matakin yin rigakafi saboda ganin yadda Ebola tana yaduwa a yammacin Afrika. An ce, gwamnatin kasar Afrika ta kudu ta dauki matakai irin daban-daban domin hana yaduwar cutar daga yammacin Afrika da suka hada da sa ido sosai kan wadanda suka ziyarci yammacin Afrika. Ban da haka kuma, filayen saukar jiragen sama na Afrika ta kudu sun kafa na'urorin binciken zafin jikin mutane da ofishin sa ido, idan an gano fasinjojin da suke zazzabi, ana ware su domin yin musu jiyya. Kazalika, gwamnatocin wurare daban-daban sun kafa runkunonin gaggawa na ba da jiyya, domin su tafi wurin da aka gano mutane da ake tababa sun kamu da cutar cikin sauri.

Bugu da kari ita ma gwamnatin kasar Birtaniya ta kira taron majalisar ministoci a wannan rana domin tattauna yadda za a tinkari wannan cuta. Ministan harkokin waje na kasar Philip Hammond ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu, babu rahoton da ya bayyana cewa akwai 'yan kasar da suka kamu da cutar ba, kuma babu wani rahoto a ketare. Amma, a ganin firaministan kasar David Cameron, ya kamata a mai da hankali kan batun. Mai ba da shawara a fannin kimiyya na gwamnatin kasar Mark Walport ya ce, gwamnati na mai da hankali kan cutar tare da daukan mataki da ya dace, sabon nau'in cuta mai yaduwa wani kalubale ne da kasashen duniya ke fuskanta, ya kamata a gudanar da aikin yin rigakafi yadda ya kamata.

An ba da labari cewa, wannan cutar ta barke a watan Maris na bana wadda ta ritsa kasashen Guinea, Laberiya da Saliyo dake yammacin Afrika. WHO ta nuna cewa, ya zuwa yanzu, ana ci gaba da fuskantar barzana a wadannan kasashen uku, daga ran 21 zuwa 23 ga wannan wata da muke ciki, karin mutane 108 sun kamu da cutar a wadannan kasashe, daga cikinsu 12 sun mutu. Dadin dadawa, ya zuwa ran 23 ga wata, wadannan kasashe uku sun sanar da adadin mutane da suka kamu da cutar da ya kai 1201, 672 daga cikinsu sun mutu.

An ba da labari cewa, Ebola ta kasance daya daga wasu cututuka da suka fi haddasa mutuwar Bil Adam a duniya, amma ba a samu mataki da za a dauka wajen warkar da ita ba tukuna. Wannan kwayar cuta tana bayyana ne kwanaki 2 zuwa 21 bayan mutum ta kamu da ita, babu shaidu dake nuna cewa wannan cuta tana yaduwa cikin iska, kullum wannan kwayar cuta tana yaduwa ta hanyar jini ko gumin jikin mutum cikin sauri, wadda za ta haddasa mummunan zazzabi da ke kisa farat daya, babbar alamar cutar shi ne zazzabi, ciwon kai, amai da gudawa da sauransu. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China