in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
WHO ta yarda da amfani da magungunan gwaje-gwaje kan cutar Ebola
2014-08-13 14:36:12 cri

Ganin yadda annobar Ebolo ta barke cikin sauri a yammacin Afirka, da yadda har zuwa yanzu ba a samu magungunan musamman na allurar rigakafin cutar ba. Game da haka, hukumar kiwon lafiya ta duniya wato WHO ta kira wani taro da ya kunshi kwararru 12 da suka fito daga kasashe daban daban, domin tattauna yiwuwar ganin ko za'a dace da ka'idojin likitanci ko a'a wajen yin amfani da magungunan gwaje-gwaje kan cutar Ebola. Mai ba da taimako ga babbar sakatariyar hukumar WHO Madam Marie-Paule Kieny ta bayyana a gun taron manema labaru cewa,

"Dukkan kwararrun suna ganin cewa, a cikin yanayin musamman na barkewar cutar a wannan karo, yin amfani da magungunan da ba a taba amincewa da su ba tukuna, a matsayin matakan da aka dauka wajen yin rigakafi da shawo kan cutar, ya dace da ka'idojin likitanci."

A makon jiya, bayan da ma'aikatan kiwon lafiya 2 na Amurka da suka kamu da cutar Ebola a kasar Liberiya suka koma gida, an yi musu allurar magungunan gwaje-gwaje da wani kamfanin kirkiro magani ya samar, sakamakon haka kuma sun samu sauki sosai. Mai yiyuwa ne, a cikin wannan yanayi na rashin samun maganin na Ebola, yin amfani da magungunan gwaje-gwaje ya zama zabi daya tak kuma fatan da muke sanyawa a kai. Domin yin la'akari kan haka ne, kwararrun hukumar WHO sun yarda da a yi amfani da magungunan gwaje-gwaje. A sa'i daya kuma hukumar WHO ta jaddada cewa, ba lallai ba ne magungunan gwaje-gwaje za su zama mai ban hadari, ban da wannan kuma, za a yi amfani da irin wadannan magungunan gwaje-gwaje ne bisa ka'idojin likitanci. Madam Marie-Paule Kieny ta bayyana cewa,

"Kwararrun sun jaddada cewa, lallai ne a yi amfani da irin wadannan magungunan gwaje-gwaje bisa ka'idojin likitanci, ciki har da bayyana yunkurin kula da masu cututtuka a fili, kuma bisa ra'ayinsu, da kiyaye bayanansu a sirri, da girmama masu cututtuka da kiyaye mutuncinsu, da shigar da al'ummomi daban daban a cikin harkar da dai sauransu. A sa'i daya kuma, kwararrun sun karfafa cewa, sabo da ba a samu cikakkun bayanai dangane da ingancin magungunan da amfaninsu, a yayin da ake amfani da su ya kamata a sauke nauyin da ke bisa wuyansu na tattara kididdiga da amfani da su tare."

A hakika dai, yanzu kusan shekaru 40 ke nan bayan da aka gano cutar Ebola, kuma ana ta kokarin gudanar da ayyukan nazari don samun magunguna da allurar rigakafinta, yayin da wasu magungunan za a iya amfani da su cikin matakai kadan, amma sai a tsaya a nan ya dade ba a samun ci gaba a aikin. Yanayin da ake ciki na tinkarar annobar Ebola, ya nuna dalilin da ya sa ake tafiyar hawainiya a kokarin samar da maganin, wato masana'antun kirkiro magunguna sun fi mai da hankali kan samun riba maimakon kawar da cutar. Game da haka, Madam Marie-Paule Kieny ta bayyana cewa,

"Dole ne mu amince da cewa, ya zuwa yanzu babu wani maganin da aka yi rajista da ke iya shawo kan cutar Ebola, wannan dai ya zama wani irin koma baya a fannin kasuwaci. An kasa samar da maganin ne ganin yadda cutar ta fi ritsar da jama'ar kasashe marasa ci gaban tattalin arziki, wadanda ba za su sanya kamfanonin magani suka samu riba ba."

Sabo da haka ne, hukumar WHO ta yi kira ga gwamnatocin kasa da kasa da hukumomin nazari daban daban da kamfanoni da su hada kansu sosai, domin ciyar da nazarin sabon magani gaba. Hukumar WHO ta yi nuni da cewa, a halin yanzu dai an riga an yi gwaje-gwaje kan allurai biyu, ana sanya ran amfani da su kafin karshen shekarar da muke ciki. (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China