in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta taimakawa kasar Saliyo wajen yaki da cutar Ebola
2014-08-14 15:54:24 cri

A halin da ake ciki cutar Ebola tana kara yaduwa a kasashe da dama da ke yammacin Afirka, cutar da tuni ta yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da dubu. A cikin wannan hali ne gwamnatin kasar Sin ta yi jigilar kayayyakin jin kai cikin gaggawa, ta kuma aike da kwararru a fannin kiwon lafiyar jama'a 9 zuwa kasashen Guinea, da Saliyo, da Liberiya, kasashen da suka fi fama da wannan cutar. Game da haka, mataimakiyar ministan harkokin wajen Saliyo Madam Ebun Strasser-King, ta bayyanawa mahalarta bikin karbar kayayyakin cewa, gwamnatin kasar Sin ta baiwa kasar tallafi a wannan mawuyacin halin da ake ciki, wanda gwamnati da jama'arta ba za su manta da shi ba.

A hakika dai, wannan ne karo na biyu da gwamnatin kasar Sin ta bayar da taimakonta, tun bayan barkewar cutar Ebola a yammacin Afirka.

Yayin da wakilinmu yake zantawa da mashawarcin kasar Sin da ke kasar Saliyo kan harkokin kasuwanci Mista Zou Xiaoming, ya gabatar da cewa, a watan Mayun bana kasar Sin ta yi la'akari da bazuwar cutar Ebola a kasar Guinea, kuma kafin gwamnatin Saliyo ta roki kasar Sin da ta bata taimako, sai kasar Sin ta ba wa Saliyo shawarar samar mata kayan tallafi. Mista Zou ya ce,

"Ya zuwa ranar 13 ga watan Mayu, kayayyaki na rukuni na farko da darajarsu ta kai kudin Sin Yuan miliyan guda sun isa kasar Saliyo, a kuma ranar 15 ga watan Mayun aka mika kayayyakin hannun gwamnatin Saliyo.

Da yake a ranar 16 ga watan Mayun ne aka gano mutum na farko da ya kamu da cutar ta Ebola, hakan ya nuna cewa kayayyakin agajin na kasar Sin sun isa ne kafin ma a kai ga gano bullar cutar ta wannan karo, sabo da haka ne kayayyakin na wancan lokaci suka bada muhimmiyar gudummawa ga Saliyo wajen yaki da cutar ta Ebola."

Mista Zou Xiaoming ya kara da cewa, bisa labarin da ya samu daga ma'aikatar kiwon lafiyar kasar Saliyo, an ce, ya zuwa ranar 12 ga watan Agustan nan, mutanen da aka tabbatar da kamuwa da cutar Ebola ya kai 703, kana daga cikin su 259 sun riga sun rasu.

A halin yanzu dai a kasar ta Saliyo, ban da yankuna biyu da ke da mutanen da su ka kamuwa da cutar ta Ebola fiye da dari, sauran yankunan ba sa fuskantar mummunan hali. A birnin Freetown babban birnin kasar Saliyo, inda jama'a ke da tarin yawa, ba a samu matsanancin bullar cutar ta Ebola ba. Mista Zou ya ce,

"A halin yanzu dai akwai mutane 12 a babban birnin kasar da suka kamu da wannan cuta, wato dai birnin Freetown dake da jama'a kimanin miliyan 2, ba wani wurin da ake fuskantar yawaitar yaduwar cutar Ebola ba, yawancin mutanen da ke kamuwa da cutar sun shigo ne daga sauran yankunan kasar domin samun magani a asibitocin dake babban birnin kasar."

Sabo da karancin ingancin tsarin kiwon lafiyar jama'a a kasar Saliyo, da kuma karancin kwarewar da hukumomin da abin ya shafa ke da shi game da dakile yaduwar cuta kamar Ebola ne, ya sa tun a farkon barkewar cutar, ta yi saurin bazuwa cikin sauri. Koda yake a baya, karkashin jagorancin hukumar kiwon lafiya ta duniya, kasar ta Saliyo ta dauki wasu matakan gaggawa, wadanda suka hada da fahimtar da jama'a illar wannan cuta ta Ebola, a sa'i daya kuma suka yi kokarin dakile bazuwar cutar.

Bisa labarin da muka samu, an ce, a halin yanzu asibitin sada zumunci tsakanin Sin da Saliyo, da kungiyar likitoci ta kasar Sin a Saliyo, na ci gaba da kokarin gudanar da aikinsu. Kuma bayan isar kayayyakin kula da lafiya da suka kai na kudin Sin Yuan miliyan 10, da zuwan kwararrun Sin masu ba da horo ga ma'aikatan kasar ta Saliyo, da kuma kaddamar da kayayyakin ga sassan dake bukatar su, ana fatan fara ganin kyautatuwar halin da ake ciki game da shawo kan cutar ta Ebola a sassan kasar. Mista Zou ya kara da cewa,

"A halin yanzu da muke la'akari da yawan jama'a da ke kamuwa da cutar Ebola, yawansu na karuwa daga kimanin 10 zuwa 20 a ko wace rana. Amma mun yi hasashen cewa, mai yiyuwa ne a halin yanzu yawansu ya kai matsayin koli, inda a nan gaba, bayan da jama'a suka kara mai da hankali kan cutar, suka kuma kara daukar matakan kandagarkinta, yawan wadanda za su iya kamuwa da cutar ta Ebola zai ragu da adadi mai yawa."(Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China