Wani jami'in a hukumar ya bayana cewa, adadin ya ragu idan aka kwatanta da yawan yaran da aka haifa a shekarar 2016. Duk da haka, yawan jariran da aka haifa a Sin shi ne a kan gaba a kasashen duniya baki daya.
Bugu da kari, ya ce, a halin yanzu, harkokin tattalin arziki da zaman al'umma su ke fi haifar da tasiri ga al'ummomin kasar ta Sin kan ko za su haihu ko a'a. kuma binciken da aka yi, ya nuna cewa, manyan dalilan da suka sa wasu 'yan kasar ba su son haihuwa su ne, yawan kudade da za su kashe wajen renon yaransu da kuma ilmantar da su, karancin hukumomin kula da yara da kuma matsin da ke kan matan kasar da dai sauransu.
Jami'in ya kuma kara da cewa, hukumar kula da harkokin kiwon lafiya da shirin kayyada iyali ta kasar Sin za ta dukufa wajen warware matsalolin da al'ummomin kasar Sin suke fuskanta a fannin haihuwa da kuma renon yara, ta yadda za a daidaita tsarin al'ummar kasa yadda ya kamata. (Maryam)